Magana Ta Fito: Dalilin da Ya Sa APC Ta Sauya Tsohon Gwamna da Sauran 'Yan Takara 25
- An samu jerin sunayen 'yan takarar da jam'iyyar APC ta sauya sunayensu duk da nasarae da suka samu a zaben fitar da gwani
- 'Yan takarar dai sun hada da na kujerun sanatoci da majalisar wakilai wadanda jimillar adadinsu ya kai mutum 26 ciki har da tsohon gwamna
- Majiyoyi sun bayyana cewa ba haka nan kawai jam'iyyar APC ta dauki matakin sauya sunayen 'yan takarar ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Baya ga rahoton kwamitin daukaka kara na zaben fitar da gwani, an gano 'kwararan’ dalilan da suka sa kwamitin NWC na jam’iyyar APC ya cire tsohon gwamnan jihar Benue, Sanata Gabriel Suswam daga cikin 'yan takara.
Kwamitin NWC ya kuma cire sunan tsohon dan majalisar wakilai na jihar Ondo, Gbenga Elegbeleye da wasu ‘yan takarar majalisar dokoki ta kasa guda 23.

Source: Facebook
Jaridar The Punch ta ce an kuma cire wasu 'yan takarar sanata guda biyar da 'yan takarar majalisar wakilai guda 19, wadanda suka yi nasara a zaben fitar da gwani na jam'iyyar da aka gudanar a watan Mayu, inda aka canza su a jerin sunayen na karshe.
Jihohin da lamarin ya shafa sun hada da Kogi, Abia, Benue, Taraba, Ondo, Niger, Kwara, Kaduna da Ebonyi.
An aike da jerin sunayen ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), ta hanyar wata wasika da shugaban APC na kasa, Nentawe Yilwatda da sakataren jam'iyyar na kasa, Ajibola Basiru, suka sanya wa hannu.
Meyasa APC ta sauya sunayen 'yan takara?
Jam'iyyar ta ce sabon jerin sunayen ya fito ne sakamakon rahoton kwamitin daukaka kara na zaben fitar da gwani.
Sai dai, Vanguard ta gano a ranar Laraba, 1 ga watan Yunin 2026 cewa, shirin mayar da ikon jam'iyyar a jihohi ga gwamnoni da manyan masu ruwa da tsaki shi ne ya janyo aka ajiye wasu daga cikin 'yan takarar a gefe.

Kara karanta wannan
Sojoji sun ceto daliban da aka sace a Borno bayan ritsa 'yan ta'addan ISWAP cikin daji
Alal misali, wata majiya mai tushe a jam’iyyar bisa sharadin boye sunanta, ta bayyana cewa Gabriel Suswam yakin neman ikon jihar Benue tsakanin sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume, da Gwamna Hycinth Alia ne ya ritsa da shi.
"An sadaukar da Suswam ne domin a faranta wa Akume rai."
- Wata majiya
Ba wa gwamnonin jihohi iko
Domin dakile fushin da ke kara ruruwa game da jerin sunayen 'yan takarar APC a jihohi da dama, an gano cewa jam'iyyar ta bai wa gwamnoni iko a fannin rarrabawa da cike takardun INEC da 'yan takara ke yi a halin yanzu.
Duk da cewa kwamitin NWC ya mika takardun na INEC ga kwamitocin gudanarwa na jhohi (SWCs), 'yan takarar da ke samun goyon bayan gwamnoni da manyan masu ruwa da tsaki a jihohin da ba na APC ba ne kawai ke da yuwuwar samun takardun.
An ce wannan na daya daga cikin dalilan da suka sa ba a buga cikakken jerin sunayen 'yan takarar ba tukuna.

Source: Facebook
Bincike ya nuna cewa Shugaba Bola Tinubu ya cika alkawarin da ya dauka na ba gwamnonin jihohi damar cin gashin kansu wajen kayyade 'yan takarar jam'iyyar a jihohinsu, wata dabarar da ta sanya tsarin rarraba takardun ya dogara kacokan a kan amincewar gwamnoni.
Da majalisar APC ya rasa kujerarsa
A wani labarin kuma, kun ji cewa wani dan majalisar dokokin jihar Delta, ya rasa kujerarsa bayan ya tsallaka daga jam'iyyar APC zuwa NDC.
Majalisar dokokin jihar Delta ce dai ta ayyana kujerar, Hon. Collins Ebgetamah, a matsayin wacce babu kowa a kanta.
Hakazalika, majalisar dokokin ta kuma bukaci akawunta da ya sanar da hukumar INEC cewa babu wanda yake kan wannan kujera a yanzu.
Asali: Legit.ng

