Gwamnan Ekiti Ya Hadu da Tinubu, Ya Fadi Adadin Kuri’un da Mutanesa Za Su Ba APC
- Gwamnan jihar Ekiti ya kai wa Bola Ahmed Tinubu ziyarar farko tun bayan lashe zaben da ya samu nasara mai kwari
- Biodun Oyebanji ya dauki alwashin ganin shugaban kasar da APC sun samu kuri’u 600, 000 zuwa 700, 000 a zaben badi
- Gwamnan ya kuma dage da kokari wajen hada kai da sauran abokan hamayyarsa wajen ganin cigaban jihar Ekiti
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
FCT, Abuja - Biodun Oyebanji ya yi hasashen nasarar jam’iyyar APC a babban zabe mai zuwa da za a yi a farkon shekarar 2027.
Ba iyaka nasarar jam’iyyarsu ta APC ba, Gwamnan jihar Ekiti ya yi wa Bola Ahmed Tinubu alkawarin kuri’u masu yawan gaske.

Source: Getty Images
Gwamnan Ekiti ya hadu da Bola Tinubu
The Nation ta ce Biodun Oyebanji ya ziyarci Shugaban Najeriya a Fadar Aso Rock a birnin Abuja, kuma ya tabo har da maganar zaben shugaban kasa.
Mai girma gwamnan ya samu rakiyar shugaban masu rinjaye a Majalisar dattawa, Opeyemi Bamidele.
Oyebanji yake cewa ya ga haske a takarar tazarcen Bola Tinubu, ya tuna da kuri’u 187, 000 da shi ya samu a zaben gwamna na farko a 2022.
Gwamnan ya ce bayan watanni shida, a lokacin shi kuma bai dade a ofis ba, sai Tinubu ya yi takara, kawai sai ga kuri’un APC sun kai 210, 000.
A zaben 2026 da shi gwamna Oyebanji ya yi nasara kuwa, ya tashi da kuri’u kusan 318, 000 saboda haka yake ganin zuwa badi labari zai canza.
"Saboda haka idan ka lissafa daga wannan, za ka ga cewa burinmu a 2027 shi ne tsakanin kuri’u 600, 000 da 700, 000, kuma wannan mai yiwuwa ne.
Idan ya samu yadda yake so, kuri’un APC a zaben shugaban kasa mai zuwa za su tashi daga 201, 000 zuwa 700, 000 wato karin 500, 000 kan na takarar 2023.

Source: Getty Images
Abubuwan da za su taimaki APC a zabe
The Sun ta rahoto gwamnan yana cewa wasu abubuwa biyu ne suka taimaka ya lashe zaben jihar Ekiti da ya gudana a cikin karshen watan Yunin 2026.
A takarar 2027, Oyebanji yana da ra'ayin cewa wadannan abubuwa ne za su yi tasiri wajen nasarar APC.
"Ba maganar abubuwa na dabam da na yi ba ne. Maganar abubuwa biyu ne: falalar Ubangiji da kuma goyon bayan shugaban kasa da ya taimaka mana muka cika alkawarin da muka yi wa al’umma.
"Takara ta kare lokacin da aka ayyana wanda ya yi nasara. Na kira saura ‘yan takaran biyu, kuma mun ziyarce daya daga cikinsu tare da shugaban yakin neman zabe na.
"Da zarar na koma Ekiti, zan ziyarci gudan. Sun yi mani alkawarin ba ni hadin-kansu domin an gama zabe, siyasa ta kare, dole mu maida hankali wajen aiki."
- Gwamnan Ekiti
Cikin abin da ya fada wa manema labarai, har da goyon bayan kafa ‘yan sandan jihohi a Najeriya.
Seriake Dickson ya zauna da Rabiu Kwankwaso
Ba a wuce awanni da haduwarsu ba, an sake ganin Sanata Henry Seriake Dickson ya taka zuwa gidan Rabiu Musa Kwankwaso kamar yadda aka ji rahoto.

Kara karanta wannan
NDC: Yaron Atiku ya nemi ADC, PDP da sauran jam’iyyu su taya Obi da Kwankwaso fada
Dickson ya yi karin haske game da ganawarsa da Kwankwaso a gidan tsohon gwamnan na Kano lokacin da ake fama da matsalar soje rajistar jam'iyyar NDC.
Henry Seriake Dickson ya yi wa Sanata Kwankwaso bayani cewa an daura sunansa a shafin INEC a matsayin 'dan takarar mataimakin shugaban kasa.
Asali: Legit.ng

