Kotu Ta Yanke Hukuncin Kisan Kan Dan Sandan Da Ya Halaka Lauya a Legas

Kotu Ta Yanke Hukuncin Kisan Kan Dan Sandan Da Ya Halaka Lauya a Legas

  • Wata babbar kotun jihar Legas ta yanke wa ɗan sanda ASP Drambi Vandi hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa laifin kashe Barr. Bolanle Raheem
  • Vandi ya harbe Bolanle Raheem har lahira a gaban mijinta yayin da take dawowa daga coci a ranar Kirsimeti a shekarar 2022
  • An samu ɗan sandan da aka dakatar da laifin kashe Bolanle, wacce ke ɗauke da juna biyu a lokacin

Jihar Legas - Babbar kotun jihar Legas ta yanke wa Drambi Vandi, wanda ya halaka lauya Bolanle Raheem a jihar Legas, hukuncin kisa ta hanyar rataya.

A ranar Litinin, 9 ga watan Oktoba, alƙalin kotun Ibironke Harrison ya samu ɗan sandan da laifin kisan kai, cewar rahoton Premium Times.

Kotu ta yanke hukuncin kisa kan dan sandan da ya kashe Bolanle Raheem
Kotu ta yankewa Vandi hukuncin kisa kan kashe Bolanle Raheem Hoto: Festus Ogun
Asali: UGC

Kotu ta ce a rataye Vandi

Rahoton jaridar Channels tv ya tabbatar da hukuncin da alƙalin ya yanke.

Kara karanta wannan

Abokai 5 Sun Mutu Tare a Mummunan Hadari a Hanyar Zuwa Daurin Aure

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamansa:

"Kotu ta samu wanda ake tuhuma da laifin aikata kisan kai. Za a rataye ka ta wuya har sai ka mutu.”

Wacce tuhuma ake yi wa ɗan sandan?

Ana zargin Vandi da harbe Raheem a kusa da kusa yayin da ita da wasu ƴan uwanta suke kan hanyar komawa gida daga hidimar coci a ranar 25 ga Disamban 2022.

Ƴan Najeriya da dama sun firgita da kisan lauyan wacce a lokacin take ɗauke da juna biyu. Marigayiya Bolane Raheem ta kuma bar yarinya ƴar shekara biyar a duniya.

ƙungiyar lauyoyin Najeriya (NBA) da ƙungiyoyin kare hakkin ɗan Adam sun bukaci a yi adalci kan kisan lauyan.

Ya musanta tuhumar da ake masa

An kama wanda ya yi harbin, Vandi, kuma an tsare shi a gidan yari bayan aukuwar lamarin. A watan Janairu, ya musanta aikata laifin kisan kai da ake zarginsa da shi.

Kara karanta wannan

Kamfanin NNPC Ya Yi Martani Kan Ba Da Kwangiloli Ga Wasu Shafaffu Da Mai A Arewa Cikin Sirri, Ya Fayyace Komai

Har ila yau, wani rahoto da jaridar The Nation ta fitar a watan Mayu, ya ce Vandi ya bayar da shaida domin kare kansa, inda ya musanta harbin lauyan.

Wanda ake tuhumar ya ce shi ne ya jagoranci tawagar ƴan sintiri ta jami'ai uku, wadanda suka tsaya gadar ƙasa ta Ajah da ke Legas, domin binciken ababen hawa a ranar da lamarin ya auku.

Wanda Aka Yankewa Hukuncin Kisa Ya Aike Da Sako Ga Gwamna

A wani labarin kuma, matashi mai shekara 25 da aka yankewa hukuncin kisa a jihar Borno, ya aike ga wasiƙa zuwa ga gwamna Babagana Umara Zulum.

Mustapha Abubakar ya buƙaci gwamnan da ya sanya hannu kan hukuncin kisan da aka yanke masa, bayan wanda ya yi garkuwa da shi ya mutu hannunsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel