Shehu Sani Ya Yi Allah Wadai Da Ma Su Daukar Mataki Kan Zargin Satar Mazakuta A Abuja

Shehu Sani Ya Yi Allah Wadai Da Ma Su Daukar Mataki Kan Zargin Satar Mazakuta A Abuja

  • Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani ya soki mutanen da ke daukar mataki kan zargin satar mazakuta a Abuja
  • Sani ya bayyana cewa abin bakin ciki ne da rashin bin doka kawai ana zargin mutum a kan karya
  • A makon da ya gabata, jami'an 'yan sanda sun cafke mutane 14 kan zargin yada jita-jitar satar mazakuta a Abuja

Jihar Kaduna - Sanata Shehu Sani ya yi Allah wadai da masu daukar doka a hannunsu kan wadanda ake zargi da satar mazakuta.

Sani na magana ne musamman a birnin Tarayya Abuja da abin yanzu ya yi kamari, Legit ta tattaro.

Shehu Sani ya yi Allah wadai da masu daukar fansa kan satar mazakuta
Shehu Sani Ya Yi Martani Kan Ma Su Daukar Mataki Kan Zargin Satar Mazakuta. Hoto: Shehu Sani.
Asali: Facebook

Meye Shehu Sani ya ce kan satar mazakuta?

Sanatan ya bayyana haka ne a shafinsa na Twitter a yau Asabar 7 ga watan Oktoba.

Kara karanta wannan

Za a Tsare Mawaka, Naira Marley da Sam Larry na Kwana 21 a Kan Mutuwar Mohbad

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce yadda mutane ke daukar doka a hannunsu abin takaici ne duk da akwai hanyoyin korafi da dama.

Wannan magana ta Sanatan na zuwa ne bayan fusatattun matasa sun kai farmaki kan jami'in dan sanda da ke ofishin 'yan sanda na yankin Gwagwa a Dei-Dei da ke birnin Abuja.

Rahotanni sun tabbatar cewa jami'an 'yan sanda sun je kwato wani ne mai suna Mubarak da aka kusa hallaka shi saboda zargin satar mazakuta.

Shehu Sani ya ce:

"Zargin satar mazakuta na kara yawa a birnin Tarayya Abuja, abin takaici da rashin bin doka shi ne yadda jama'a ke daukar mataki kan wanda ake zargi.
"Babu wani kimiyya da ta tabbatar da haka, kawai matsafa ke jefa mutane cikin wannan hali."

Wane mataki 'yan sanda su ka dauka kan satar mazakuta?

Kara karanta wannan

Wakilin Jihar Kaduna Ya Fadi Ana Kokarin Tantance Sababbin Ministoci a Majalisa

A makon da ya gabata ne jami'an 'yan sanda su ka kama mutane 14 bisa zargin yada labarai na karya kan satar mazakuta a Abuja.

Rundunar ta ce sun kama mutanen ne bayan tabbatar da labarin da su ke kawo wa karya ne wanda ke haddasa rasa rayuka.

Shehu Sani ya yabawa BUA kan rage kudin siminti

A wani labarin, tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani ya yabawa kamfanin BUA kan rage farashin siminti a kasar.

Sanatan ya ce wannan abin a yaba ne inda ya bukaci masu siyar da abinci su yi koyi da kyawawan halayen BUA.

Asali: Legit.ng

Online view pixel