Abba Gida Gida Ya Kaddamar Da Rabon Kayan Tallafi Karo Na Biyu A Kano

Abba Gida Gida Ya Kaddamar Da Rabon Kayan Tallafi Karo Na Biyu A Kano

  • Abba Gida Gida ya kaddamar da shirin rabon kayan tallafi ga mabukata a karo na biyu a jihar
  • Gwamnan ya ce kayan abincin an ware su ne kawai don marasa karfi da ke fadin jihar baki daya
  • Ya gargadi mambobin kwamitin da 'yan jaridu da jami'an tsaro kan taba kayan inda ya ce ba dan su aka kawo ba

Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya kaddamar da rarraba kayan tallafin abinci ga marasa karfi a jihar.

Gwamnan ya bayyana haka ne a shafinsa na Twitter inda ya ce wannan shi ne karo na biyu na raba kayan tallafin.

Abba Gida Gida ya raba kayan tallafin abinci karo na biyu a Kano
Abba Gida Gida Ya Gargadi Mambobin Kwamiti Kan Taba Kayan Tallafi. Hoto: @Kyusufabba.
Asali: Facebook

Meye Abba Kabir ya ce kan kayan tallafin?

Ya ce wannan karo za a raba buhunan abinci 387,200 ga unguwanni 484 da ke fadin jihar.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Sace Malamin Musulunci Yayin Da Su Ke Raka Gawa Makabarta, Bayanai Sun Fito

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan ya kara da cewa gwamnatin za ta samar da bas bas don taimakawa mata da kuma shirin samar da tasi na ba da jimawa ba.

Ya ce:

"A jiya na samu damar kaddamar da raba kayan tallafi ga masu kananan karfi a karo na biyu.
"A wannan karo, za a rarraba buhunan abinci har 387,200 ga Unguwanni 484 da ke fadin jihar Kano.
"Za mu kuma samar da bas bas da za su taimakawa mata da kuma tasi don saukakawa jama'a nan ba da jimawa ba."

Yaushe Abba Kabir ya kaddamar da rabin a Kano?

A jiya Litinin, 9 ga watan Oktoba aka kaddamar da shirin rabon kayan na tallafi a karo na biyu da zai kunshi kananan hukumomi 44 da ke jihar, cewar Punch.

Da ya ke jawabi, Gwamna Abba Kabir ya gargadi mambobin kwamitin kan almundahana da kayan wanda aka ware don masu kananan karfi.

Kara karanta wannan

"Mu Na Daf Da Durkushewa", NNPC Ya Tura Sako Ga Tinubu Kan Cire Tallafi Mai A Kasar

Ya ce kayan an ware su ne don masu kananan karfi inda ya ce mambobin kwamitin da 'yan jaridu da kuma jami'an tsaro kayan ya haramta a gare su.

Abba Gida Gida ya biya wa dalibai kudin makaranta

A wani labarin, Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya biya wa wasu daliban Jami'a kudin makaranta.

Gwamnan ya ce ya yi hakan ne don taimaka musu samun shaidar kammala karatunsu a Jami'o'in.

Ya ce Jami'o'in sun hada da Bells da Al-Qalam da kuma Igbenidion wanda gwamnatin baya ta yi watsi da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.