Kocin Kungiyar Kwallon Kafa Ya Sha da Kyar kan Zargin Satar Mazakuta

Kocin Kungiyar Kwallon Kafa Ya Sha da Kyar kan Zargin Satar Mazakuta

  • ‘Yan sanda a Rivers sun ceto wani kocin kwallon kafa da aka fi sani da Gaso bayan wasu jami’an OSPAC kan wasu zarge-zarge
  • Bidiyon da ya yadu ya nuna an daure hannayen Gaso tare da dukan sa da yi masa tambayoyi bayan wani mutum ya yi zargin bacewar mazakutarsa
  • Iyalan Gaso da masu kare hakkin bil’adama sun bukaci a sako shi tare da gurfanar da mambobin OSPAC da suka kai masa hari.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Port Harcourt, Rivers - Rundunar yan sanda a Rivers sun ceto wani kocin kwallon kafa mai suna Gaso daga hannun wasu ƴan sa-kai.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa an ceto shi ne bayan wasu mambobin kungiyar sintiri ta OSPAC sun kama shi tare da yi masa duka.

An ceto ran matashi kan zargin satar mazakuta
Sufeta-janar na ƴan sanda, Olatunji Rilwan Disu. Hoto: Nigeria Police Force.
Source: Twitter

An zargi wani da satar mazakuta

Kara karanta wannan

Bayan mutuwar jigo a Izala, tsohon shugaban APC ya rasu a hannun yan bindiga

Wani bidiyo da Punch ta samu ya nuna an daure hannayen Gaso yayin da wasu ke yi masa tambayoyi tare da muzanta shi.

Lamarin ya faru ne a Igwuruta da ke karamar hukumar Ikwerre bayan wani mutum ya zarge shi da haddasa bacewar mazakutarsa ta hanyar sihiri.

Mutumin da ya yi korafin ya ce Gaso ya nemi kudin mota zuwa Okrika, amma ya ki ba shi kudi kai tsaye.

Ya ce ya yi niyyar biya masa kudin sufuri a tashar mota, amma daga baya ya lura cewa mazakutarsa ta bace.

A cikin bidiyon da ake ta yadawa, Gaso ya musanta zargin gaba daya, yana mai cewa bai taba neman kudin daga mutumin ba da har zai yi masa wannan zargi.

Wani dan uwansa mai suna Solomon Ogan ya ce sun garzaya ofishin ‘yan sanda bayan samun labarin kama shi da aka yi.

Ogan ya bayyana cewa mambobin OSPAC sun yi wa Gaso mugun duka tare da jikkata kansa kafin ‘yan sanda su shiga tsakani.

An ci zarafin wani da ake zargi da satar mazakuta
Taswirar jihar Rivers da ake zargin wani da satar mazakuta. Hoto: Legit.
Source: Original

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta magantu

Kara karanta wannan

Yadda aka nemi ceto malamar Islamiyya amma mutane suka taru suka kashe ta

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Centre for Basic Rights Protection and Accountability Campaign ta yi Allah wadai da lamarin.

Mai kula da kungiyar, Prince Wiro, ya ce azabtarwa da nuna mutum a bainar jama’a ya saba wa hakkokin dan Adam.

Ya bayyana cewa iyalan Gaso sun tabbatar da cewa ya samu munanan raunuka sakamakon dukan da aka yi masa.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Rivers, Grace Iringe-Koko, ta tabbatar da cewa jami’ansu sun ceto mutumin daga hannun jama’a.

Ta ce yanzu haka yana karkashin kariyar ‘yan sanda yayin da ake ci gaba da bincike kan abin da ya faru, cewar Daily Post.

An hana ƴan sanda yin TikTok, Facebook

A wani labarin, an ji cewa rundunar ƴan sandan Najeriya ta haramta wa jami’an ‘yan sanda amfani da kafafen sada zumunta.

Sabuwar dokar ta hana jami’ai wallafa bidiyo, hotuna ko shirye-shirye cikin kayan aiki na ‘yan sanda ba tare da izini ba.

Disu ya gargadi jami'an cewa karya doka zai fuskanci dakatarwa, rage mukami, hana albashi har zuwa kora daga aiki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.