An Tafka Abin Kunya Tsakanin Lauyoyi Yayin da Su Ka Yi Doke-Doke a Cikin Kotu a Jihar Enugu

An Tafka Abin Kunya Tsakanin Lauyoyi Yayin da Su Ka Yi Doke-Doke a Cikin Kotu a Jihar Enugu

  • Mutane son soki wani faifan bidiyo da aka gano wasu lauyoyi na fada da junansu a cikin kotun majistare da ke jihar Enugu
  • A cikin faifan bidiyon, daya daga cikin lauyoyin na kiran dan uwanshi da mahaukaci yayin shi ma ya ke mai da martani
  • Wannan lamari ya jawo cece-kuce inda mutane su ka nuna damuwa kan yadda mahukunta su ke a kasar da kuma lalacewar shari’a

Jihar Enugu – A cikin wani faifan bidiyo da aka yada, an gano wasu lauyoyi na fada a cikin kotun majistare da ke jihar Enugu.

Jaridar Punch ta tattaro cewa hatsaniyar ta afku ne a yau Juma’a 13 ga watan Oktoba yayin zama a kotun majistare a Nsukka da ke jihar.

Lauyoyi sun bai wa hamata iska a cikin kotu a Enugu
Yadda lauyoyi su ka bai wa hamata iska a Enugu. Hoto: Peter Mbah.
Asali: Twitter

Me ya jawo hatsaniyar tsakanin lauyoyin biyu?

Wani lauya daga ciki ya buga wa dan uwanshi kujera yayin cacar bakin ta yi kamari inda shi ma ya dauki kujera ya makawa lauyan.

Kara karanta wannan

Tinubu Na Shawarar Kirkiro Kotun Musamman Domin Daure Barayin Gwamnati

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An jiyo daya daga cikin lauyoyin na cewa cikin harshen Turanci “Ku kalli wannan mahaukacin” inda dayan ya amsa da cewa ‘Ku kalle shi, ya yi 'bleaching' kamar wawa.”

Irin wannan ba shi ne farau ba a Najeriya inda ake samun hatsaniya irin wannan har majalisun Tarayya da na jihohi, Legit ta tattaro.

Ku kalli bidiyon lauyoyin da ke fada a kasa:

A jihar Enugun dai, kotun sauraron kararrakin zaben 'yan majalisar dokokin jiha da na tarayya ta rushe nasarar dan majalisar jiha na jam'iyyar PDP.

Rahotanni sun tabbatar cewa kotun ta rusa nasarar Okey Mbah, dan jam'iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben a mazabar Nkanu ta Gabas a majalisar jihar.

An cafke matar da ta watsa wa mijinta man gyada mai zafi a Ribas

A wani labarin, rundunar ‘yan sanda a jihar Ribas ta yi nasarar cafke matar da ta watasa wa mijinta tafasasshen man gyada a jihar Ribas

Kara karanta wannan

‘Yan Fashi Sun Yi Shigan ‘Yan Sanda, Sun Yi Satar Miliyoyin Kudi Ido Ya Na Ganin Ido

Matar mai suna Hope Nwala ta wanke mijin nata ne mai suna Nwanko bayan wata ‘yar hatsaniya da ta shiga tsakaninsu a karamar hukumar Etche.

Mijin ya bayyana cewa bai taba tsammanin ‘yar cacar bakin za ta kai matar ga aikata wannan danyen aiki ba, da ba zai fara ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel