Manyan Labarai A Yau
Abdullahi Ganduje ya amince a kara kudi domin a kammala titi a Kwankwaso. Titin da ake yi a karamar hukumar Madobi zai taimakawa mutanen tsohon Gwamnan Kano.
Ministan harkokin sufurin tarayya yace nan da mako daya mutane za su cigaba da hawa jirgin kasan Kaduna-Abuja, yanzu duk wanda bai da NIN ba zai hau jirgi ba.
Kasar Indonesiya za ta yi sabuwar doka da za ta fara hukunta masu aikata zina da zaman dadiro da wasu ababe da kasar ke ganin sun ci karo da al'ada da tarbiya.
Yan majalisa a zauren majalisar kasar Senegal sun ba hammata iska a zauren majalisa a ranar Alhamis yayin da ake gabatar da kasafin kudin ma'aikatar shari'a .
Wani direban mota ya taro rikici bayan da ya sheke wani mutum garin tserewa a gidan mai bayan da aka siyar masa mai. Ana zaton ba zai biya kudi ba, don aka.
Dalibin kwallejin ilimi a jihar Bauchi mai suna Kamaludeen Musa ya halaka abokinsa kuma dan ajinsu mai suna Usman Umar da wuka yayin da rikici ya shiga tsakani.
Jiang Zemin, tsohon shugaban China wanda ake yi wa kallon wanda ya habaka kasar ta zama cikin manyan kasashen duniya masu fada a ji ya riga mu gidan gaskiya.
Wani hazikin dan Najeriya ya gina bandaki mai samar da iskar gas na amfani wurin girki na gida da kuma wutar lantarki. Mutane da dama a soshiyal midiya sun yaba
A yayin da ta je majalisa, Ministar kudi ta bayyana gaskiyar abin da ya sa aka yi cushen N1.7tr a kasafin 2023, an ji karin da aka gani bai nufin an saba doka.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari