An Ja Kunnen Malamai kan Yi wa 'Yan Siyasa Kamfen a Masallaci a 2027

An Ja Kunnen Malamai kan Yi wa 'Yan Siyasa Kamfen a Masallaci a 2027

  • Shugaban hukumar JAMB a Najeriya, Farfesa Ishaq Oloyede ya yi nasiha ga malamai game da tallata 'yan siyasa a zaben 2027 da ke tafe
  • Ishaq Oloyede ya yi magana ne yayin wani taro da aka yi a masallacin Lekki da ke jihar Legas domin tattauna matsalolin da suka shafi Musulunci
  • Bayanan shi na zuwa a daidai lokacin da 'yan siyasa ke shirye-shiryen neman takara a 2027, inda suke dab da fara yakin neman zabe a jihohi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Legas - Shugaban JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede ya gargadi malaman addinin Musulunci da kada su yi amfani da masallatai da mimbari wajen yin kamfen a babban zaben 2027.

Oloyede, wanda kuma shi ne Sakatare Janar na Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA), ya ce dole ne limamai su fifita hadin kai da kira ga shugabanci nagari a cikin al’ummominsu.

Kara karanta wannan

Jakadanci: Fani Kayode ya faɗi dalilin neman Tinubu ya dauke shi daga turai zuwa Afirka

Farfesa Ishaq Oloyede yayin lakca a Legas
Farfesa Ishaq Oloyede yana gargadin malamai kan tallata 'yan siyasa. Hoto: Lekke Central Mosque
Source: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa Oleyede ya bayyana hakan ne a taron shekara-shekara na limamai wanda kungiyar Lekki Muslim Ummah ta shirya a Babban Masallacin Lekki da ke Legas.

Nasiha ga malamai kan kamfen

Taron mai taken “Limami, Siyasa da Shugabanci,” ya samu halartar limamai da malamai sama da 400 daga Legas da sauran sassan kasar nan.

Oloyede ya ce ya kamata masallatai su ci gaba da kasancewa cibiyoyin shiryar da jama'a da hadin kai maimakon wuraren gudanar da siyasa da jawo rarrabuwar kawuna.

“Bai kamata limamai su yi amfani da mimbari wajen goyon bayan jam’iyya ko yakin neman zabe ba. Maimakon haka, su rika wayar da kan mabiyansu, su jagorance su kan harkokin zamantakewa,”

In ji shi.

Ya kara da cewa ya kamata shugabannin addini su taimaka wa masu ibada wajen fahimtar hakikanin siyasa da yanke shawara mai kyau kan wanda za su zaba ba tare da tilasta musu ra’ayinsu ba.

Kara karanta wannan

Dan majalisar Amurka ya harzuka kan harin Plateau, ya gayawa Trump matakin dauka kan Najeriya

Oloyede ya kuma gargadi mutane kan sayen kuri’u da mayar da siyasa hanyar neman kudi, yana mai cewa hakan kawo matsala a shugabanci da kuma rusa kyawawan dabi’u.

Masallacin Lekki da le Legas
Babban masallacin Juma'a na Lekki a jihar Legas. Hoto: Lekki Central Mosque
Source: Facebook

Maganar Farfesa Alaro a taron

A wata lacca mai taken “Matsayin Shari’a Kan Kada Kuri’a,” Farfesa Abdul-Razzaq Alaro na Jami’ar Ilorin ya bukaci Musulmi su ci gaba da shiga harkokin zabe domin kada a mayar da su saniyar ware.

Rahoton Muslim News ya nuna cewa ya ce shiga siyasa ya yi daidai da koyarwar Musulunci domin kada a bar Musulmi a baya.

Shi ma da yake jawabi, Babban Limamin Babban Masallacin Lekki, Ridwanullahi Jamiu, ya bayyana Musulunci a matsayin cikakken tsarin rayuwa da ya kunshi shugabanci, tattalin arziki da zamantakewa.

Shugaban kungiyar LEMU, Abdulganiyu Labinjo, ya ce an shirya taron ne domin shiryar da limamai kan harkokin addini da kuma al’amuran zamani yayin da ake tunkarar zaben 2027.

Gwamnoni sun fitar da 'yan takara

A wani labarin, mun kawo muku cewa wasu gwamnonin jihohi da za su sauka a mulki a 2027 sun fara bayyana wadanda za su gaje su.

Kara karanta wannan

Matar da APC ta tsaida takara a Katsina ta fara fuskantar cikas daga malaman Musulunci

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno ya bayyana Mustapha Gubio a matsayin wanda yake fata ya gaje shi a zaben 2027.

A jihar Gombe, gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya zabi Dr Jamilu Isiyaku Gwamna a cikin sama da mutum 10 da suka nuna suna son su gaje shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng