An Gano Gawar Wani Ɗan Kasuwa A Cikin Dakin Otel A Bauchi

An Gano Gawar Wani Ɗan Kasuwa A Cikin Dakin Otel A Bauchi

  • Yan sanda a jihar Bauchi sun gano gawar wani dan kasuwa mai suna Mr Chukwunonso Chukwujekwu a dakin otel
  • Hakan ya faru ne bayan matarsa mai suna Mrs Grace Chukwujekwu ta kai rahoton batansa caji ofis yan sandan suka bazama bincike
  • Kafin rasuwar Chukwujekwu, babban sarkin garin Boi, Mallam Bala Likita ya masa sarautar Kaigaman Boi

Jihar Bauchi - An tsinci gawar wani dan kasuwa mai shekara 37, Mr Chukwunonso Chukwujekwu a unguwar Tudun Wada da ke Boi, karamar hukumar Bogoro a jihar Bauchi.

Daily Trust Saturday ta tattaro cewa marigayi Chukwunonso dan asalin karamar hukumar Anambra East ne a jihar Anambra, amma yana zaune kuma yana kasuwanci a kauyen Boi.

Bauchi Map
An Gano Gawar Wani Dan Kasuwa A Cikin Dakin Otel A Bauchi
Asali: UGC

Kafin rasuwarsa, babban sarkin Boi, Mallam Bala Likita ya nada shi sarautar Kaigaman Boi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wani mamba na Police Community Relations Committee, PCRC, a yankin, Joel Daniel ya ce mazauna garin sun shiga rudani kan yanayin mutuwarsa.

Daniel ya yi bayanin an tsinci gawar marigayin a otel bayan an kai wa PCRC da yan sandan Bogoro rohoton cewa ya bace, rahoton The Punch.

Da aka tuntube shi, kakkakin yan sandan jihar Bauchi, SP Ahmed Wakil ya tabbatar da lamarin kuma ya ce kwamishinan yan sanda ya umurci a yi bincike kan mutuwarsa.

Yadda yan sanda suka gano gawar Mr Chukwujekwu

SP Wakili ya ce:

"Wata Mrs Grace Chukwujekwu, yar shekara 27, ta kai rohoto ofishin yan sanda na Bogoro a ranar 30 ga watan Nuwamban 2022 cewa mijinta, Mr Chukwunonso Chukwujekwu, ya bar gida don zuwa shagonsa a Boi amma tun lokacin bai dawo gida ba.

"Bayan ta shigar da rahoton, DPO na Bogoro ya jagoranci yan sanda sun fita bincike. Daga bisani, an gano gawarsa a wani otel da ke Tudun Wada a Boi, karamar hukumar Bogoro yana kwance a kasa kumfa na fita daga bakinsa."

Wakil ya kara da cewa an dauki shi an kai Babban Asibitin Bogoro inda likita ya tabbatar ya mutu kuma kwamishinan yan sandan ya umurci a yi binciken sanadin mutuwarsa yayin da ake cigaba da bincike.

An Gano Gawar Jarumar Fim Ta Najeriya A Dakin Otel Sati Daya Bayan Ta Yi Bikin Birthday

Yan sanda a jihar Binuwai sun gano gawar wata jarumar fina-finai mai suna Takor Veronica a wani dakin otel a jihar, rahoton The Nation.

Rahotanni mabanbanta sun ce an gano gawar Veronica ne kimanin sati daya bayan yin bikin zagoyowar ranar haihuwarta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel