'Dan Wasan Damben Najeriya Ya Yanke Jiki Ya Faɗi Matacce Ana Tsaka Da Dambe

'Dan Wasan Damben Najeriya Ya Yanke Jiki Ya Faɗi Matacce Ana Tsaka Da Dambe

  • Chukwuemeka Igboanugo, dan damben wasan 'boxing' da ke wakiltar Jihar Imo a gasar wasanni na kasa da ke gudana a jihar Delta ya riga mu gidan gaskiya
  • Igboanugo ya yanke jiki ya fadi ne a cikin filin wasan damke a lokacin da suke fafatawa da takwararsa Prince Gaby Amagor na Anambra a yau Talata
  • Wata majiya daga hukumomin shirya wasar ta ce Amagor ya yi wa Igboanugo wani naushi ne nan take ya fadi kasa kuma alkalin zabe ta dakatar da wasar, aka garzaya da shu asibiti a can likitoci suka tabbatar ya cika

Jihar Imo - Wani dan wasan dambe a gasar wasanni na kasa da ake yi a halin yanzu a Asaba, babban birnin jihar Delta ya rasu, Daily Trust ta rahoto.

Dan damben wasan boxing, Chukwuemeka Igboanugo, wanda ke wakiltar Imo, ya rasu bayan ya sha kaye hannun Prince Gaby Amagor daga jihar Anambra a rukunin masu daukin kilogiram 86.

Kara karanta wannan

An Kama Hatsabibin Dan Damfara A Bauchi Da Katin ATM 31, Ya Fallasa Yadda Ya Ke Sace Kudin Bayin Allah

Boxing
Bikin Wasannin Kasa: Dan Wasan Damben Najeriya Ya Yanke Jiki Ya Fadi Matacce Ana Tsaka Da Dambe. The Guardian
Asali: Facebook

Alkalin wasa ya tsayar da damben bayan da Igboanugo ya kasa tashi bayan naushinsa

An naushi Pascal a kunchinsa hakan yasa alkalin wasa ya tsayar da damben lokacin da ya gaza tashi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wani jami'in damben, wanda ya nemi a sakayya sunansa ya shaida wa wakilin Daily Trust cewa:

"Nan take aka fitar da shi daga filin damben saboda bashi kulawa kafin a garzaya da shi asibiti inda aka tabbatar ya rasu."

An fara gasar wasannin na kasa ne na wannan shekarar a makon da ta gabata a jihar Delta.

Wasan da za a shafe wata guda ana yi shine madadin wasannin Olympics a Najeriya, rahoton Within Nigeria.

Dukkan jihohin kasar 36 da babban birnin tarayya Abuja sun tura yan wasa da za su wakilce su a wasanni daban-daban.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Dakta Aliyu Tilde, Kwamishinan Ilimi na Jihar Bauchi Yayi Murabus, Ya Sanar da Dalili

Dan Wasan Kwallon Najeriya Ya Yanke Jiki Ya Fadi Ya Ce Ga Garinku Ana Tsaka Da Wasa

A wani rahoto mai kama da wannan, kun ji cewa wani matashi dan shekara 31 shima ya yanke jiki ya fadi matacce yayin da ya ke tsaka da kwallo a Lekki, jihar Legas.

Lamarin mai bakanta rai ya faru ne a ranar 2, 2 ga watan Oktoban shekarar 2022 kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Matashin da ba a tabbatar da sunansa ba yana bin kwallo ne kwatsam sai ya yanke jiki ya fadi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel