Gwamnan Shahararriyar Jihar Najeriya Ya Bayyana Addinin Ya Zamto Mafi Samun Sabbin Mabiya A Jiharsa

Gwamnan Shahararriyar Jihar Najeriya Ya Bayyana Addinin Ya Zamto Mafi Samun Sabbin Mabiya A Jiharsa

  • Gwamnan jihar Anambra ya magantu kan addinin da ya fi sauran samun mabiya a jihar Anambra
  • A cewar Farfesa Chukwuma Soludo, addinin bautan gumaka ya zama sabon addini da ke tashe a jiharsa
  • Tsohon gwamnan na babban bankin Najeriya, CBN, ya bukaci coci ta tashi ta yaki 'makiyin' kafin ya lalata jihar

Jihar Anambra - Gwamna Chukwuma Soludo na jihar Anambra ya bukaci coci ta tashi tsaye ta yaki addinin bautan gumaka da ya bayyana a matsayin addini mafi saurin girma a jihar.

Da ya ke magana a wurin wani taron addini a Onitsha, Soludo ya ce ya daura damarar yaki da bata-gari, wuraren bautansu da bokayensu kuma ya kone gumakansu tun bayan da ya zama gwamna a jihar, Vanguard ta rahoto.

Soludo
Soludo Ya Bayyana Addinin Da Ya Zamto Mafi Samun Sabbin Mabiya A Anambra, Ya Umurci Coci Ta Dauki Mataki. Hoto: Charles Chukwuma Soludo.
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Gwamnan ya ce:

"Za su iya zuwa da duk abin da za su yi, amma da Bibul a hannun daman mu, za mu yi nasara."
"Anambra na hannun Ubangiji, dole mu cigaba da addu'a, mu kwato jihar mu daga bata-gari, yan daba da saba doka.
"Bautan gumaka shine addini mafi saurin bazuwa a jihar kuma ba zai yi wu mu zuba ido ba.
"Idan muka hada kai, za mu tsira tare, amma idan muka raba kanmu, za mu mutu a rarrabe. Wannan kasar mu ne, kada mu karaya kan wannan."

Soludo ya aika da sako zuwa ga coci

Da ya ke bayyana Anambra a matsayin jiha ta Ubangiiji, Soludo ya ce akwai bukatar dukkan darikun kiristoci su hada kai, yana mai cewa banbancin da ke tsakaninsu kawai na hanyar bauta ne, Daily Trust ta kara.

Soludo ya bawa mutanen jihar tabbacin cewa zai cigaba da tafiya tare da dukkan kungiyoyin addinai sahihai tare da nada mukami bisa cancanta.

Soludo ya kara da cewa:

"Mu zama canjin da muke son gani. Anambra za ta cigaba da habbaka."

MURIC Ta Yi Martani Kan Haramta Mini Skirt A Makarantu

A bangare guda, kungiyar kare hakkin musulmi ta MURIC ta jinjinawa gwamnan jihar Anambra Charles Soludo saboda hana saka gajerun sket a makarantun gwamnati da masu zaman kansu a jiharsa.

Farfesa Ishaq Akintola, shugaban MURIC ya ce haramtawar ta yi daidai da yancin mata musulmi na saka hijabi a Najeriya.

MURIC ta ce matakin ya nuna gwamnan yana da hangen nesa da kishin kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel