Bidiyon Yadda Wani Direba Ya Sha Mai a Gidan Mai Ya Ki Biyan Kudi, Garin Gudu Ya Kashe Wani

Bidiyon Yadda Wani Direba Ya Sha Mai a Gidan Mai Ya Ki Biyan Kudi, Garin Gudu Ya Kashe Wani

  • Wani direba ya kashe wani mutum a jihar Kaduna a kokarin da yake na tserewa biyan kudin mai N3000 da ya sha a gidan mai
  • Bayan siyan mai, an ce direban ya tsere a guje ba tare da biya ba, inda ya kauce ya kai ga buge wani mutum da ke gefe ya mutu
  • A bidiyon da aka gani na yadda lamarin ya faru, jama'a da dama sun yi martani, Sarkin Mota ne ya yada bidiyon a Twitter

Kaduna - Wani direban da ba a bayyana sunansa ba ya yi kokarin tserewa bayan da ya sha man N3000 a gidan mai, inda ya lalata wasu ababen hawa tare da kashe mutum daya da ke kan hanya.

Wannan mummunan yanayi ya faru ne a jihar Kaduna da daren ranar Talata 29 ga watan Nuwamban 2022.

Kara karanta wannan

Ba sauki: Yadda uba ya nade diyarsa cikin jakar leda saboda ta yi masa kashi a jikinsa

Sarkin Mota, wani ma'aboci Twitter da ya bayyana kansa a matsayin mataimakin dan takarar gwamnan PDP a jihar kan harkokin yada labarai ne ya yada bidiyon a kafar sada zumunta.

Yadda direba ya sheke wani garin gudun biyan kudin mai
Bidiyon Yadda Wani Direba Ya Sha Mai a Gidan Mai Ya Ki Biyan Kudi, Garin Gudu Ya Kashe Wani | Hoto: @alamin_ghost
Asali: Twitter

Ya rubuta cewa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Direba ya siya man 3k jiya da dare sai ya fece a guje ba tare da ya biya ba, daga baya motar ta fi karfinsa ta buge wasu motocin da ke wurin, abin takaici hakan ya kai ga mutuwar wani. Allah ya jikanshi."

Kalli bidiyon:

Martanin jama'a a Twitter

Bayan ganin wannan bidiyon a Twitter, mutane da dama sun bayyana martaninsu kan lamarin mara dadi.

Ga kadan daga ciki min tattaro muku:

@KabeerZayyan yace

"Mai siyar da man ne ya hau gaban motar yana kokarin kwace matukinta daga hannun direban hakan ne yasa aka yi hatsarin. Za ku iya ganin mutumin a makale a gaban motar a farkon bidiyon. PS: Ya rasa ransa, direban kuma ya tsira."

Kara karanta wannan

Matsala A Sansanin Yan Bindiga A Yayin Da Yan Sanda Suka Kama Mai Musu 'Asiri' Dan Shekara 53

@gtex50 yace:

"A kan 3k, wannan ya tuna min da lamari irin wannan a baya can a Maiduguri, direban ya tsere shi kuwa mai siyarwan ya rike matukin motar. Sakamakon dai bai yi dadi ba, direban ya mutu a hatsarin. Kada kuke wasa da rayuwa kan abin da bai kai ya kawo ba."

@abecent yace:

·Allah ya jikan shi, ya mutu a hanyar da ta dace."

@FUgbem yace:

"Dole sai ka tuka mota??Idan baka da kudin siya ka ajiye motar a gida ka bi sahunmu na tattaki cikin kwanciyar hankali."

Yadda aka janye dokar da aka sanya wa 'yan adaidaita sahu a Kano

A wani labarin kuma, an sanya dokar hana 'yan adaidaita sahu bin wasu manyan hanyoyi a jihar Kano, lamarin da ya kai ga cece-kucen jama'a.

Ana cikin rikicin ne gwamnati ta sanar da janye dokar bayan duba da koken al'umma da kuma abin da suke cewa.

Kara karanta wannan

Abu Mai Sosa Zuciya: Hotunan Wani Matashi Bai Ci Abinci Ba Tsawon Kwana 2 ya Samu Taimako

Ana yawan samun cece-kuce a jihar Kano kan abubuwan da suka shafi 'yan adaidaita sahu da hukumar zirganiyar ababen hawa ta KAROTA.

Asali: Legit.ng

Online view pixel