"Ba Bayan Gida, Babu Girki": Dan Najeriya Ya Gina Bandaki Mai Samar Da Iskar Das Don Girki Da Wutar Lantarki

"Ba Bayan Gida, Babu Girki": Dan Najeriya Ya Gina Bandaki Mai Samar Da Iskar Das Don Girki Da Wutar Lantarki

  • A yayin da mutane ke kokawa kan karuwar kudin iskar gas a kasar, wani dan Najeriya ya samo zabi
  • Mutumin ya gina bandaki da ke samar da iskar gas tare da lantarki dan kansa, ta hanyar amfani da shara
  • Hotunan kirkirar da ya yi mai kayatarwa sun dauki hankulan mutane a shafukan sada zumunta

Wani dan Najeriya mai hazaka ya gina bandaki da ke samar da iskar gas na girki da wutar lantarki da kansa.

Bekwarra Blog, wanda ya wallafa labarin a shafin impressive news a dandalin Facebook na Rant HQ Extention, ya bayyana cewa wannan fasahar tana da sauki kuma ta fi dadewa.

Bandaki mai samar da gas da lantarki.
"Ba Bayan Gida, Babu Girki": Dan Najeriya Ya Gina bandaki Mai samar da iskar gas don girki da wutar lantarki. Hoto: Bekwarra Blog.
Asali: Facebook

Hotunan mutumin yayin da ya ke gina bandakin kuma yana amfani da shi ya dauki hankulan masu amfani da dandalin sada zumunta.

Kara karanta wannan

Hotunan yadda matashi ke samar da wutar girki da ta lantarki daga toroso ya girgiza jama'a

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Legit.ng ta tattaro cewa sunan mutumin Okwudor kuma dan asalin karamar hukumar Njaba na jihar Imo ne.

Masu amfani da shafukan intanet sun yaba da hazakarsa sun nemi lambarsa.

Wasu daga cikin abubuwan da masu amfani da soshiyal midiya suka ce

Dickson ya ce:

"Abin takaici ne ganin yan Najeriya da dama sun san fasahar sarrafa makamashi na biogas musamman wadanda suka karanci physics da chemistry a makarantu.
"Mai zai hana su dage su yi wani abu kan hakan su cece mu daga tsadar kudin gas.
"Yanzu idan zaka cika tukunyar gas mai girman 12.5kg sai ka kashe N9500. Kuma galibi baya kai wata guda. Gaskiya muna bukatar mafita daga wannan rayuwa mai wahala."

John Aduku ya ce:

"Makamashi wanda kai iya narkewa a kasa. Ba sabon abu bane, tafi kasashen Afirka ta Gabas ka ga yadda fiye da kashi 50 na kasar ke amfani da shi.

Kara karanta wannan

Gwamnan Babban Jihar Arewa Ya Faɗa Wa Ƴan Najeriya Wanda Ya Cancanta Su Zaɓa Shugaban Kasa A 2023

"Ya kamata karkara a Najeriya su rungume shi."

Maryqueen Osita Blessing ta ce:

"Eh, an kowa mana a makaranta a darashin biotechnology... a tsangayar genetics and biotechnology a Unical."

Chinenyenwa Chigbu Eno ta ce:

"Takwara ta mace ta gina irin wannan biogas din, amma nata na amfani da kashin kaji don samar da gas din girki."

Mavis Marvelous Mavis ya ce:

"Yanzu wato idan ba ka yi bayan gida ba girki kenan."

Wani dan Najeriya mai basira ya kera gangariyar mota da N80,000 kacal

Najeriya na tattare da mutane masu basira da hazaka. Hakan yasa a lokuta daban-daban za ka rika mamakin ganin abin da ake kerawa a kasar.

Duk da cewa ana alakanta kere-kere da kudade masu yawa, a wasu lokutan ana iya amfani da kalilan din kudi don kera abu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel