Za A Fara Ɗaure Mazinata Da Masu Zaman Dadiro A Gidan Yari A Indonesiya

Za A Fara Ɗaure Mazinata Da Masu Zaman Dadiro A Gidan Yari A Indonesiya

  • Gwamnatin kasar Indonesiya za ta aiwatar da wasu sabbin dokoki da za su kawo sauyi a zamantakewar mutanen kasar
  • A cikin kunshin dokokin da ake sa ran majalisar kasar za ta ratabba hannu a kai a Disamba akwai na hukunta mazinata, masu zaman dadiro, masu zagin shugaban kasa dss
  • A yan shekarun baya, gwamnatin kasar ta so aiwatar da dokokin amma ta dakatar saboda rashin amincewa da su daga al'umma

Indonesiya - Za a fara hukunta mazinata, inda za a iya yanke musu hukuncin daurin tsawon shekara daya ga duk wanda aka samu da laifin, rahoton Reuters.

Ana fatan majalisar kasar za ta amince da sabbin dokokin a watan Disambar shekarar 2022.

Majalisar Indonesiya
Za A Fara Ɗaure Mazinata Da Masu Zaman Dadiro A Gidan Yari A Indonesiya. Hoto: REUTERS/Beawiharta
Asali: AFP

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari a wani masallaci a jihar Delta, inda da dama suka jikkata

Wasu abubuwa da ke kunshe cikin sabbin dokokin sun hada da:

  • zaman namiji da mace tare ba da aure ba
  • zagin shugaban kasa ko hukumomin kasa
  • bayyana ra'ayoyi da suka ci karo da muradin kasa
  • zubar da juna biyu, sai dai kawai ga wadanda ta hanyar cin zarafi suka yi cikin
  • yin 'asiri ko tsafi'

A wani hira da ya yi da Reuters, mataimakin ministan shari'a na kasar, Edward Omar Sharif Hiariej, ya ce dokokin an yi su ne bisa tsarin 'al'adun Indonesia'.

An yi watsi da kudirin da ya gabata

An yi watsi da wani yunkurin da aka yi a baya na zartar da sabon kundin laifukan a 2019, a yayin da shugaban kasar Indonesiya Joko Widodo , wanda aka fi sani da Jokowi, ya ce damuwa da al'umma suka nuna kan wasu sassan.

A lokacin, Jakarta Post ta ruwaito cewa majalisar dokokin Indonesia ta fuskanci mummunan martani game da wasu abubuwa masu rikitarwa a cikin dokar da aka gabatar wanda zai haramta abubuwa da ake yi wa kallon ba laifi bane yayin da yake barazana ga 'yancin jama'a na bayyana ra'ayinsu, da sirri.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: CAN ta zargi wata hukuma da cinye kudin hajjin kiristoci a kasar nan

Sai dai kuma, kwanaki hudu kafin a zartar da daftarin kudirin, Jokowi ya dakatar da shari’ar.

Mai hukunta mazinata ya sha bulala bayan samunsa da laifin zina

Wani mutum na asalin kasar Indonesiya da ke aiki a majalisar malamai na garin Aceh ya shiga hannun hukuma bayan samunsa da laifin zina.

Mutumin mai suna Mukhlis ibn Muhammad dan shekara 28 yana cikin wadanda ke dabbaka shari'ar musulunci a garin na Aceh, BBC Hausa ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel