Gwamnatin Ganduje Za Ta Karasa Titi Zuwa Kauyen Kwankwaso da Wasu Ayyuka a Kano

Gwamnatin Ganduje Za Ta Karasa Titi Zuwa Kauyen Kwankwaso da Wasu Ayyuka a Kano

  • Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya amince a kara kudin aikin titin Kwanar Kwankwaso zuwa Kwankwaso
  • Titin da ake gyarawa a karamar hukumar Madobi zai taimakawa mutanen Rabiu Kwankwaso wanda ya yi Gwamna
  • Kwamishinan yada labarai yace an amince da kwangilolin wasu ayyuka da za ayi a kananan hukumomin da ke Kano

Kano Majalisar zartarwa ta jihar Kano ta amince da canjin kudi da aka samu wajen kwangilar hanyar Kwanar Kwankwaso-Kwankwaso a Madobi.

Jaridar Leadership tace kwangilar titin nan da aka bada a farkon shekarar nan a kan N372.268 ya kara kudi, gwamnatin Kano za tayi cikon N97.826m.

Tuni an biya N154.491m, kuma har aikin ya kai rabi domin 'yan kwangila sun yi 50% a garin da tsohon Gwamnan jihar, Dr. Rabiu Kwankwaso ya fito.

Da ya zanta da manema labarai bayan taron majalisar zartarwa da aka yi a garin Kano, Kwamishinan yada labarai yace an sake duba kwangilar.

Kudin aiki ya tashi saboda tsadar kaya

An rahoto Malam Muhammad Garba yana cewa yawan tashin farashin kayan gine-gine ya jawo kudin da za a kashe wajen aikin ya karu, ya kai N470m.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Muhammad Garba ya sanar da manema labarai cewa Gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta amince a fitar da N40.373m domin samar da hasken wuta.

Gwamnan Kano
Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje Hoto: @aaibrhim1
Asali: Facebook

Za ayi amfani da kudin ne domin gyara ban-dakoki da ke kasuwanni kauyuka a jihar Kano. Akwai ban dakin kasuwanni 72 da suke amfani da hasken rana.

Aikin da ake yi a yankin Hotoro

Kwamishinan ya nuna za a amince da canjin kudin aikin da aka samu na katafaren titin Muhammadu Buhari da ake ginawa a kan titin zuwa Maiduguri.

Garba yace aikin ya kai 97%, har an bude gadojin sama da kasa ga wadanda ke bi ta hanyar. Za a kashewa aikin N9.231bn saboda CCTV, katanga da ciyawa.

A rahoton Channels TV, an fahimci za a fadada kwalejin koyon aikin tsabta domin a rika koyar da sababbin ilmomin da hukumar NBTE ta bada dama a kawo.

Za ayi amfani da filin SUBEB da ke Sabuwar Kofa a matsayin bangaren makarantar. Baya ga haka an amince a biya wasu alawus ga malaman jami’ar YMS.

Zanga-zanga a New Nigeria Peoples Party

Rahoto ya nuna 'Dan takaran Majalisa ya bayyana Sulaiman Othman Hunkunyi a matsayin wanda zai kashewa ‘Yan jam’iyyar NNPP kasuwa a zabe.

Wasu sun ce idan da hali, NNNP ta canza ‘dan takaran Gwamnan jihar Kaduna, idan ba haka ba zai yi wahala jam’iyya mai kayan dadi ta kai labari a badi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel