Wani Dalibi Kamaludeen Dan Shekera 22 Ya Caka Wa Abokinsa, Usman, Wuka Har Lahira A Bauchi

Wani Dalibi Kamaludeen Dan Shekera 22 Ya Caka Wa Abokinsa, Usman, Wuka Har Lahira A Bauchi

  • Jami'an tsaro sun kama wani dalibi mai shekaru 22 mai suna Kamaludeen Musa kan zargin kashe abokinsa Usman Umar
  • Rahotanni sun nuna cewa dambe aka yi tsakanin Kamaludeen da Usman saboda Kamaludeen ya tafi wani wuri ba tare da sanar da abokinsa ba
  • A yayin fadan ne Kamaludeen ya daba wa Usman wuka a cikinsa bayan ya masa rauni a dan yatsa kamar yadda wasu shaidu yan makarantar kwalejin ilimi ta Kangere suka tabbatar

Jihar Bauchi - Yan sanda a jihar Bauchi sun kama wani Kamaludeen Musa, dan shekara 22, kan zarginsa da kashe abokinsa, Usman Umar, dan shekara 25.

Kamar yadda Leadership ta rahoto, Kamaludeen da Usman dalibai ne na kwalejin ilimi da ke Kangere a jihar Bauchi.

Wanda ake zargi
Wani Dalibi Kamaludeen Ya Caka Wa Abokinsa, Usman, Wuka Har Lahira A Bauchi. Hoto: Leadership Nigeria.
Asali: Facebook

Sanarwar da kakakin yan sanda, Ahmed Mohammed Wakil ya fitar, wacce yan jarida a Bauchi suka samu kwafi a ranar Laraba, ta ce rashin jituwa ya faru tsakaninsu kan wani fita gabanin afkuwar lamarin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar kakkakin yan sandan, a ranar 28 ga watan Nuwamban 2022, misalin karfe 1 na rana, bayanai da rundunar yan sanda ta samu ya nuna a ranar misalin 9.15 na safe, Kamaludeen Musa ya caka wa abokinsa, Usman Umar, wuka mai kaifi a cikinsa.

Wakil ya ce bayan isan su wurin, yan sanda sun dauki wanda abin ya faru da shi zuwa Asibitin Kwararru na Bauchi idan likita ya tabbatar ya mutu, yayin da aka kama wanda ake zargin, Vanguard ta rahoto.

Binciken farko da yan sanda suka fara yi ya nuna wanda ake zargin da wanda abin ya faru da shi abokai ne kuma suna ajin karshe a Kwalejin Ilimi na Tafawa Balewa da ke karamar hukumar Kangere jihar Bauchi.

Yadda lamarin ya faru

Ya yi bayanin cewa:

"Karamin rikici ya barke tsakaninsu lokacin da marigayin ya yi korafin wanda ake zargin ya tafi wani wuri ba tare da sanar da shi ba, hakan yasa suka fara dambe inda aka raunata wanda ake zargin a yatsarsa, shi kuma ya ciro karamin wuka daga aljihunsa ya caka wa marigayin a cikinsa kamar yadda ganau biyu suka jaddada; Musa Danjuma dan shekara 22 da Nawasi Sadi dan shekara 20 duk daliban makarantar."

Wakil ya kara da cewa ana cigaba da zurfafa bincike kan lamarin.

Matar Aure Ta Caka Wa Mijinta Wuka Har Lahira Lokacin Da Ya Ke Kokarin Neman Hakkinsa Na Aure

A wani rahoton daban, wani bawan Allah mai suna Olamilekan Salaideen ya riga mu gidan gaskiya sakamakon caka masa wuka da matarsa, Odunayo, ta yi a lokacin da ya ke neman ta bashi hakkinsa na kwanciyar aure.

Kakakin yan sandan jihar Oyo, SP Adewake Osifeso ya yin da ya ke gabatar da wasu wadanda ake zargi ga manema labarai ya ce ba a dade da sulhunta tsakanin ma'auratan ba sai wannan abin ya faru.

Asali: Legit.ng

Online view pixel