Amurka Ta Saki Sunayen Kasashe Masu Tauye Ƴancin Addini (Cikakken Jerin Sunaye)
Kasar Amurka ta fitar da sunayen wasu kasashen duniya da ta kira masu tauye hakkin addini. Sakataren Amurka, Antony Blinken ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar.
A Disambar 2020, Amurka ta saka Najeriya cikin kasashe da ta saka cikin jerin 'masu keta hakkin yin addini'.
Amma bayan shekara guda, an cire Najeriya daga jerin kasashen.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Binciken ya fitar da jerin sunayen kasashen bisa gwargwadon matakin abin da ake zarginsu da aikatawa.
Kasashen da ke take hakkin addini a cewar sanarwar ta Amurka sune.
- Burma
- Jamuhuriyar Al'ummar China (Sin)
- Cuba
- Eritrea
- Iran
- Nicaragua
- DPRK
- Pakistan
- Rasha
- Saudiyya
- Tajikistan
- Turkmenistan
Sunayen kasashe masu keta hakkin addini na musamman
- Algeria
- The Central African Republic
- Comoros
- Vietnam
Kungiyoyi da aka sa wa ido na musamman
- Al-Shabab
- Boko Haram
- Hayat Tahrir al-Sham
- Houthis
- ISIS-Greater Sahara
- ISIS-Afirka ta Yamma
- Jama'ar Nusrat al-Islam wal-Muslimin
- Taliban
- The Wagner Group
Sanarwar da Blinken ta kara da cewa:
"Sanarwar da muka fitar na sunayen ya dace da al'adarmu da muradunmu na kare tsaron kasa da hakkan hakkin yan adam a duniya. Kasashen da ke kare hakkin bil adama sun fi zaman lafiya, kwanciyar hankali da cigaba kuma sune suka fi zama kawayen Amurka fiye da wadanda ba su yi kare hakokin.
"Za mu cigaba da sa ido kan yancin addini a kowanne kasar duniya tare da kare hakkin wadanda ake musgunawa saboda addininsu. Za kuma mu cigaba da tattaunawa da kasashen kan batun yancin addini ko suna jerin ko ba su ciki.
"Muna maraba da dukkan gwamnatocin kasashe don tattaunawa kan dokoki da abubuwa da suka ci karo da dokokin kasa da kasa don cire su daga jerin."
Yar Najeriya Ta Zama Janar Din Soja A Amurka
A wani rahoto, Amanda Azubuike, wata yar asalin Najeriya ta kafa tarihi bayan an mata karin girma zuwa Birgediya Janar a rundunar sojojin Amurka a Fort Knox, jihar Kentucky, Amurka.
Amanda haifafiyar Landan ne a Birtaniya kuma ta shiga aikin soja a shekarar 1994 ta zama matukiyar jirgin sama bayan cin jarrabawa.
Shugaban rundunar sojin Amurka, Janar James Rainey ya ce Azubuike ta kawo cigaba ga duk wadanda ke aiki tare da ita.
Asali: Legit.ng