Karin Farashin Tikiti da Tsare-tsare da Za a Kawo a Jirgin Kasan Kaduna-Abuja

Karin Farashin Tikiti da Tsare-tsare da Za a Kawo a Jirgin Kasan Kaduna-Abuja

  • Gwamnatin tarayya tace nan da mako daya mutane za su cigaba da hawa jirgin kasan Kaduna-Abuja
  • Ministan sufuri ya bada sanarwar cewa sai da lambar waya da NIN za a iya sayen tikitin jirgin kasan
  • Baya ga dabarun da aka kawo, hukumar NRC za ta kara farashin tikitin jirgin nan da wani ‘dan lokaci

Abuja - Gwamnatin tarayya tace nan da kwanaki bakwai za a cigaba da amfani da jirgin kasan Kaduna zuwa babban birnin tarayya Abuja.

The Cable tace Ministan sufuri, Mu’azu Sambo ya bayyana haka sa’ilin da ya zanta da ‘yan jarida a ranar Lahadi, 27 ga watan Nuwamba 2022.

Bayan an yi tunanin jiragen za su dawo aiki a makon nan, Mu’azu Sambo ya shaida cewa sai nan da kwanaki bakwai za a fara saida tikitin.

Kara karanta wannan

Talaka ya yi nasara: Abin da 'yan Najeriya ke cewa bayan da Aisha Buhari ta janye kara kan Aminu

Ministan harkokin sufuri na kasa yace an kara lokacin ne domin fasinjoji su samu isasshen lokacin da za su saba da tsare-tsaren da za a kawo.

Dabarun da aka shigo da su

"Yanzu mun kawo sabon tsari wajen sayen tikiti.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sayen tikiti yana bukatar a bada lambar waya da kuma lambar NIN, ta haka za a fara tabbatar da tsaro.
Saboda haka duk lokacin da jirgi yake yawo daga wannan tasha zuwa wata, mun san su wanene cikinsa.
Jirgin kasa
Jirgin kasa Hoto: www.nannews.ng
Asali: UGC
Idan ba ka da lambar NIN, ba za ka hau jirginmu ba, iyakar ta kenan.
Muddin karamin yaro ne, matashi zai yi maka rajista, kuma babban mutum ba zai iya yi wa kananan yara fiye da hudu rajista ba."

- Mu’azu Sambo

Za a kara farashin tikiti

A wani rahoto da Punch ta fitar, an ji Ministan yana cewa za a kara farashin tikiti a dalilin yadda abubuwa suke kara tsada a halin yanzu a Najeriya.

Kara karanta wannan

Jami'iyar APC Nakasu Kawai Ta Kawo A Nigeria Tsawon Lokacin da ta Shafe Tana Mulki, Atiku

Mu’azu Sambo bai yi bayanin lokacin da hukumar NRC za tayi wannan kari ba, amma ya tabbatar da za a rage adadin jigilar da yake yi a duk rana.

Siyasar 2023

Dazu muka samu labari Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ba ta da wanda zai tsaya mata takarar Gwamna da ‘Dan Majalisa a jihar Ogun.

A lokacin da zabe ya karaso, sai ga shi Alkalin babban kotun tarayya ya haramtawa ‘Yan takara fiye da 20 neman kujerar mulki saboda saba dokar zabe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel