An Ba Hammata Iska A Majalisa Bayan Ɗan Majalisa Ya Sharara Wa Takwararsa Mari

An Ba Hammata Iska A Majalisa Bayan Ɗan Majalisa Ya Sharara Wa Takwararsa Mari

  • An yi dambe a zauren majalisar kasar Senegal a ranar Alhamis 1 ga watan Disamba kan maganganun da yar majalisa ta yi kan wani malamin addinin musulunci
  • Yar majalisa Amy Ndiaye ce ta furta maganganu marasa dadi kan malamin, Serigne Moustapha Sy, mai goyon bayan jam'iyyar hamayya
  • Hakan yasa wani dan majalisa ya sharara mata mari, ita kuma ta jefe shi da kujera yayin da wasu yan majalisa suka ba hammata iska

Senegal - Yan majalisa sun ba hammata iska tare da jifan juna da kujeru a zauren majalisar Senegal a ranar Alhamis kan abin da ake yi wa kallon cin mutunci ga wani shugaban addini mai goyon bayan yan hamayya.

Dan majalisar na jam'iyyar hamayya ya mari yar majalisa Amy Ndiaye bisa kalamanta, kamar yadda hotuna na talabijin da soshiyal midiya suka nuna kuma AFP ta tabbatar da sahihancinsu, Daily Trust ta rahoto.

Yan Majalisa
'Yan Majalisa Sun Ba Hammata Iska A Zauren Majalisar Senegal. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ta mayar da martani ta hanyar jifansa da kujera sannan ta fadi kasa, inda wasu yan kungiyar ta suka taimaka mata ta tashi.

Daga nan sai aka yi naushe-naushe tsakanin yan majalisar kafin kakakin majalisar ya dakatar da zaman.

Rikicin ya barke ne yayin kada kuri'a kan kasafin kudin ma'aikatar shari'a na shekarar 2023.

Dalilin faruwar rikici a majalisar

Maganganun da Ndiaye ta yi game da Serigne Moustapha Sy, shugaban musulmi wanda ke goyon bayan yan hamayya amma shi ba dan majalisa bane, ya haifar da rikicin, Reuters ta rahoto.

A ranar 27 ga watan Nuwamba, ta zarge shi da 'yin amai ya lashe' kuma da cin mutuncin Shugaba Macky Sall, a cewar rahotanni daga kafafen labarai.

Dan majalisa Abba Mbaye ya fada wa gidan talabijin cewa yan majalisa na jam'iyyar hamayya ba za su amince a cigaba da zaman majalisar ba 'har sai matar ta bada hakuri.'

Wasu mambobin kungiyoyi tare da masu karre hakkin mata sun yi tir da harin da aka kai wa Ndiaye, wanda ya dace da kamfe da suke yi kan yaki da cin zarafin mata da yara.

An fara zaben Shugaba Sall ne a 2012 na tsawon shekara 7 sannan aka sake zabensa na tsawon shekara biyar a 2019.

Kawo yanzu bai bayyana shirinsa ba kan zaben shugaban kasa na gaba da za a yi a 2024.

Yan Majalisa Sun Ba Hammata Iska A Senegal

Yan majalisa sun yi dambe a ranar Laraba yayin da ake zaman majalisa lokacin da ake tattauna batun sauya tsarin zaben kasar.

A wani bidiyo da ya bazu a soshiyal midiya, an hangi yan majalisar wakilai daga jam'iyyar Sierra Leone Peoples Party mai mulki da babban jam'iyyar hamayya suna musayar naushi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel