Manyan Labarai A Yau
Surukin Gwamnan Kano ya fadawa Kotu kayan da matarsa, Balaraba Ganduje ta shiga dida ta dauke. Nan da ranar 19 ga watan Junairun nan za a cigaba da shari’a.
Alkalin alkalai na jihar Oyo, Munta Abimbola ya saki wata dattijuwa yar shekara 65 da jikanta dan shekara 15 da aka tsare a gidan yari kan satar kaji 2 a Oyo.
Shugaban APC na kasa, Abdullahi Adamu ya kaddamar da yakin neman zaben APC a Benuwai, yana ganin sauya-shekar da Gwamna Samuel Ortom tamkar sace masu kuri'a ne.
Hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Legas ta sanar da rasuwar wani bawan Allah da ba a bayyana sunansa ba wanda ya nutse a ruwa yayin da ya tuka babur din ruwa
Wale Adeniran, jagora kuma ciyaman na kungiyar masu son kafa kasar yarbawa ta Ilana Omo Oodua Worldwide ya yi murabus daga kujerarsa don bada daman yin bincike.
Rundunar yan sandan Najeriya reshen jihar Bauchi sun kama wata mata yar shekara 50 mai suna Amina Guguwa kan zarginta da kashe kishiyarta Amina Koli yayin dambe
Vladimir Putin na Rasha ya umurci a tsagaita wuta na wucin gadi a yakin da kasarsa keyi da Ukraine don bada dama yin bikin kirsimetin masu kiristancin gargajiya
Fitaccen mawakin Najeriya, Habeeb Okikiola, wanda aka fi sani da Portable ya burge masayansa yayin wani wasa da ya yi a Fatakwal a tsakiyar rafi a jihar Ribas.
Masarautar Bauchi ta kori Bello Kirfi, tsohon ministan ayyuka na musamman kuma Wazirin Bauchi daga sarautarsa kan abin da ta kira 'rashin biyayya' ga gwama
Manyan Labarai A Yau
Samu kari