Kamfanin Rano Air Ya Dakatar da Sufurin Jiragensa zuwa Wasu Jihohi a Najeriya
- Kamfanin sufuri na Rano Air ya nuna damuwa kan tsadar man jirgin sama, wanda ya tashi da sama da 300% a Najeriya
- Sakamakon haka ne kamfanin ya sanar da dakatar da zirga-zirgan jiragensa a wasu hanyoyi na 'dan takaitaccen lokacin saboda tsadar mai
- Duk da bai bayyana hanyoyin da zai dakatar da aiki na, wata majiya ta ce Maiduguri da Gombe na cikin wadanda matakin zai shafa
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Kamfanin jiragen sama na Rano Air ya sanar da dakatar da wasu daga cikin hanyoyin zirga-zirgarsa na wucin gadi bayan tashin farashin man jiragi na Jet A1 da sama da 300%.
Ya ce hauhawar farashin man jiragen sama ya sa gudanar da sufurin jiragen sama zuwa wasu jihohi ya zama mai matuƙar wahala da rashin riba.

Source: UGC
Rano Air ya dakatar da aiki a wasu hanyoyi
Kamfanin ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, wanda aka fi sani da Twitter yau Juma'a.
Sai dai kamfanin Rano Air bai fayyace wadanne jihohi ne zai dakatar sufurin jiragensa ba a cikin sanarwar.
Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta shaida wa manema labarai cewa hanyoyin Maiduguri da Gombe na daga cikin waɗanda ake tunanin za a dakatar na ɗan lokaci.
A halin yanzu, Rano Air na zirga-zirga tsakanin Abuja, Legas, Kano, Sakkwato, Maiduguri, Kaduna, Katsina, Bauchi da Osubi.
Majiyar ta ce:
“Tabbas za a iya dakatar da sufuri a sama da rabin hanyoyin da kamfanin ?$ gudanar da ayyukansa, amma nan ba da jimawa ba mahukunta za su fitar da cikakken bayani.”
Dalilin Rano Air na daukar mataki
A cikin sanarwar, kamfanin ya ce tashin farashin man jiragen ya jefa harkokin sufuri cikin matsin lamba mai tsanani, lamarin da ya tilasta musu ɗaukar matakin dakatar da wasu hanyoyi.
Kamfanin ya nuna damuwa kan matsalolin da hakan zai iya jawo wa fasinjoji da abokan hulɗarsa, yana mai cewa an ɗauki matakin ne bayan dogon nazari domin tabbatar da tsaro, inganci da dorewar ayyuka.
Rano Air zai maida wa fasinjoji kudinsu
Rano Air ya kuma tabbatar wa da fasinjojin da suka riga suka zayi tikitin tafiya cewa za a taimaka musu wajen mayar da kuɗi, sauya lokaci ko canza hanyar tafiya.
Kamfanin ya ƙara da cewa zai dawo da zirga-zirga a hanyoyin da aka dakatar da zarar yanayi ya daidaita kuma harkokin suka koma yadda za su kasance masu anfani.

Source: Getty Images
Daily Trust ta ruwaito cewa kamfanonin jiragen sama na cikin gida sun dade suna kokawa kan tsadar man jiragen sama, har ma wasu suka yi barazanar dakatar da aiki gaba ɗaya.
Ko da yake gwamnatin tarayya ta shiga tsakani domin dakile hakan, wasu daga cikin kamfanonin sun ce har yanzu suna sayen mai kusan Naira 3,000 kan kowace lita.
An bullo da shirin lamunin hawa jirgi
A wani labarin, kun ji cewa Gwamnatin Najeriya ta bullo da wani shiri na ba da lamunin sayen tikitin jirgin sama domin saukakawa mutane zirga-zirga.
Gwamnatin ta ƙaddamar da sabon tsarin mai suna “Fly Now, Pay Later” domin bai wa ‘yan Najeriya damar yin tafiye-tafiyen jirgin sama cikin sauƙi.
Ta ce an samar da wannan tsari ne domin rage nauyin biyan kuɗin tikiti gaba ɗaya, wanda sau da yawa ke hana mutane yin tafiya a jiragen sama domin biyan bukatunsu a kan lokaci.
Asali: Legit.ng


