Wani Bawan Allah Ya Nutse A Ruwa Yayin Da Ya Ke Zura Gudu Kan 'Babur Ɗin Ruwa' A Legas

Wani Bawan Allah Ya Nutse A Ruwa Yayin Da Ya Ke Zura Gudu Kan 'Babur Ɗin Ruwa' A Legas

  • Wani bawan Allah ya riga mu gidan gaskiya sakamakon nutsewa da ya yi a ruwa yayin tuka babur din ruwa a Lekki, Legas
  • Hukumar bada agajin gaggawa na jihar Legas ta bakin sakatarenta na dindindin, Olufemi Oke-Osanyintolu, ta tabbatar da afkuwar lamarin
  • Oke-Osanyintolu ya ce jami'an hukumarsa na kokarin ciwo gawar mamacin daga ruwa kuma ya rasu ne sakamakon gudu fiye da kima da ya ke yi a babur din ruwan

Jihar Legas - An tabbatar da rasuwar wani mutum da ba a riga an bayyana sunansa ba yayin da ya ke tuka babur din ruwa a rafin Lekki-Ikoyi a jihar Legas, rahoton The Cable.

Sakataren dindindin na hukumar bada agajin gaggawa na jihar Legas, Mr Olufemi Oke-Osanyintolu, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba 11 ga watan Janairun 2023.

Kara karanta wannan

Buhari Ya Ce Ya Cika Alkawuran da Ya Dauka, Tinubu Ya Ce ba Haka Abin Yake ba

Gadar Ikoyi, Legas
Wani Mutum Ya Nutse Yayin Da Ya Ke Tuka Babur Din Ruwa A Legas. Hoto: @MobilePunch.
Asali: Twitter

Ya ce wanda abin ya faru da shi ya nutse ne sakamakon gudu da ya ke yi kan babur din ruwan, ya kara da cewa ana kokarin ciro gawarsa daga rafin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

"Masu kai daukin gaggawa na hukumar da ke bakin aiki a Lekki sun gano wani namiji baligi ya nutse a rafin Lekki-Ikoyi sakamakon gudu fiye da ka'ida da ya ke yi yayin tuka babur din ruwa a wurin."

Janar Manaja na hukumar kula da albarkatun ruwa na jihar Legas, Mr Oluwadamilola Emmanuel, shima ya tabbatarwa jaridar The Punch afkuwar lamarin.

Ya ce:

"Har yanzu ana bincike a kan lamarin. A halin yanzu ba zan iya bada bayani mai yawa ba. Zan bada karin bayani gobe da safe."

Wani Matashi Dan Shekara 18 Ya Mutu Yayin Ceto Shanunsa Daga Nutsewa a Jigawa

A wani rahoton, kun ji cewa wani matashi Adamu Musa, dan shekara 18 mazaunin Buji a karamar hukumar Buji, Jihar Jigawa ya kwanta dama sakamakon nutsewa a ruwa.

Kara karanta wannan

Da Dumi-dumi: 'Yan Bindiga Sun Yi Yunkurin Sace Shugaban Majalisar Dokoki a Jihar Arewa

Musa ya rasu ne yayin da ya ke kokarin ceto shanunsa daga nutsewa a cikin ruwar kamar yadda jaridar The Punch ta rahoto.

Adamu Shehu, mai magana da yawun rundunar NSCDC na jihar Jigawa ya tabbatar da afkuwar lamarin cikin sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel