Jakada: Fani Kayode Ya Faɗi Dalilin Neman Tinubu Ya Dauke Shi daga Turai zuwa Afirka
- Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, ya tabbatar da nadinsa a matsayin jakadan Najeriya zuwa Afirka ta Kudu
- Fani-Kayode ya ce hakan ya faru ne bayan amincewar Bola Tinubu saboda korafin da ya yi ga shugaban kasa
- Ya ce shi ne ya nemi a mayar da shi Afirka ta Kudu zuwa Jamus saboda ra'ayinsa na ɗan Afirka da kusancin manufofin ƙasashen biyu
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, ya tabbatar da sauya masa kasa a matsayin jakandan Najeriya.
Fani-Kayode ya tabbatar da cewa an nada shi jakadan Najeriya a kasar Afirka ta Kudu bayan amincewar shugaban kasa Bola Tinubu.

Source: Facebook
A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba 6 ga watan Mayun 2026 wanda ya wallafa a shafinsa na X.
Kasar da aka tura Fani-Kayode tun farko
Fani-Kayode ya bayyana cewa tun farko an tura shi kasar Jamus kafin daga baya ya nemi sauyin aiki.
Ya ce ya bukaci a mayar da shi Afirka ta Kudu saboda wasu dalilai na kashin kai da kuma dacewar manufofin kasar da ra'ayinsa na Pan-African.
Tsohon ministan ya bayyana cewa ya tattauna matsalar da ministan harkokin wajen Najeriya, Yusuf Tuggar, wanda daga baya ya kai bukatar ga shugaban kasa Bola Tinubu.
Fani-Kayode ya gode wa shugaban kasa Tinubu da Yusuf Tuggar saboda yadda suka amince da bukatarsa tare da ba shi damar yin aiki a Afirka ta Kudu.
Ya kuma yaba wa Sanata Ita Enang wanda tun farko aka tura Afirka ta Kudu, saboda amincewa da tsarin musayar mukamai tsakaninsu zuwa Jamus.

Source: Twitter
Da gaske Jamus ta ki amincewa da shi?
Sai dai Fani-Kayode ya karyata rahotannin da ke cewa gwamnatin Jamus ta yi watsi da nadinsa a matsayin jakadan Najeriya zuwa kasar Turai.

Kara karanta wannan
Wike vs Turaki: 'An ruguza yunkurin hana PDP tsaida dan takarar shugaban Kasa a zaben 2027'
Ya bayyana rahotannin a matsayin karya, sharri da kuma yunkurin bata masa suna tare da kunyata gwamnatin tarayya da shugaban kasa Tinubu.
Dan siyasar ya ce binciken farko ya nuna cewa wasu ne suka dauki nauyin wallafa rahoton domin lalata sunansa a gida Najeriya da kasashen waje.
Ya kara da cewa tuni suka kai koke ga hukumomin tsaro yayin da lauyoyinsa suka fara shirye-shiryen gurfanar da masu yada rahoton a kotu.
Fani-Kayode ya jaddada cewa babu wata takarda daga Jamus da ta nuna an ki amincewa da nadinsa, yana kalubalantar masu yada labarin su kawo hujja.
A karshe, ya ce yana fatan fara aiki a Afirka ta Kudu, kasar da ya bayyana a matsayin abar koyi kuma mai tarihin da ke karfafa kasashen Afirka.
Fani-Kayode ya musanta zargin Tinubu da kisa
Mun ba ku labarin cewa tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Femi Fani-Kayode, ya musanta zargin cewa ya taba alakanta Shugaba Bola Tinubu da kisan kai.
Ya ce Omoyele Sowore ne ya yi amfani da wata tsohuwar magana tasa domin kare kansa a karar batanci da ake yi masa.
Fani-Kayode ya bukaci Sowore ya janye kalamansa ko ya fuskanci shari’a, yana mai yabawa salon jagorancin Tinubu.
Asali: Legit.ng
