Dandazon Masoya Sun Dira Ribas a Fatakwal Yayin Da Portable Ya Yi Waka A Tsakiyar Rafi, Bidiyon Ya Bazu

Dandazon Masoya Sun Dira Ribas a Fatakwal Yayin Da Portable Ya Yi Waka A Tsakiyar Rafi, Bidiyon Ya Bazu

  • Mawakin nan mai yawan tada hayaniya a baya-bayan nan ya yi wasa a Fatakwal kuma ya kayatar da masoyansa
  • Mai wakan na Zazu ya wallafa bidiyon lokacin da ya yi waka kan wani abu da aka saka a tsakiyar rafi a jihar
  • Mutane da dama sun yi ta tofa albarkacin bakinsa game da bidiyon da Portable ya wallafa mai kayatarwa

Fatakwal - Fitaccen mawakin Najeriya Portable ya shiga sabuwar shekara da wani salo mai kayatarwa kamar yadda bidiyon da ya wallafa a shafinsa ya nuna.

Mawakin na Zazu ya yi wasa a Fatawkwal kuma ya fita daban da sauran wasannin da ya saba yi a baya.

Portable
Dandazon Masoya Sun Dira Ribas a Fatakwal Yayin Da Portable Ya Yi Waka Kan Ruwa, Bidiyon Ya Bazu. Hoto: @portablebaeby
Asali: Instagram

Portable ya wallafa bidiyon da ke nuna shi lokacin da ya iso gefen rafi tare da masu taya shi waka da masu shirya casu.

Kara karanta wannan

Ikon Allah: Wani Mutumi Ya Sauya Fasalin Keke Napep Ta Koma Kamar Jirgi, Bidiyon Ya Ja Hankali

Daga nan aka shigar da mawakin da tawagarsa cikin jirgin ruwa don kai su 'mimbarin' waka da aka kafa a tsakiyar rafi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bayan ya dare kan 'mimbarin', mawakin ya cigaba da wakarsa cikin kuzari da kayatarwa, wasu masoya sun shiga rafin don su matsa kusa su gan shi.

Kalli bidiyon a kasa:

Masu amfani da soshiyal midiya

young_smith231 ya ce:

"Wannan mutumin yana da kyauta, albarkar da yawa ta ke. Ba kowa ne zai iya samun kudi kamar Davido ko Wizkid ba, ka cigaba da lalabawa kana karbar kudinka."

codykenkzz ya ce:

"Gaskiya wannan babban lamari ne, mimbarinsa kan ruwa, shine ya fara wannan."

thevillageboibrand ya ce:

"Ba su son Portable amma mutumin ya yi wasanni fiye da 30 a wannan shekarar ko fiye."

akorede_dd ya ce:

"Shine mawakin Najeriya na farko da ya fara wasa a tsakiyar rafi, mutane sun shiga cikin ruwan don su kalle shi, lallai kai mawaki ne mai son wahala."

Kara karanta wannan

Babban Malamin Addini Ya Bayyana Wanda Zai Ci Zaben Shugaban Kasa Na 2023 A Najeriya

Yan sanda sun bukaci Portable ya kai kansa ofishinsu cikin gaggawa ko su kama shi

A wani rahoton, rundunar yan sandan Najeriya reshen jihar Ogun ta umurci shahararren mawaki, Habeeb Okikiola, wanda aka fi sani da Portable ya kai kansa ofishinsu mafi kusa.

Yan sandan sun bada wannan umurnin ne bayan da wani tsohon DJ dinsa suna DJ Chicken ya yi kararsa kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel