Mijin 'Yar Gwamna Ganduje Ya Sanar da Kotu Babban Laifin da Mai Dakinsa Ta Tafka

Mijin 'Yar Gwamna Ganduje Ya Sanar da Kotu Babban Laifin da Mai Dakinsa Ta Tafka

  • An cigaba da sauraron karar Inuwa Uba da mai dakinsa Asiya-Balaraba Ganduje a wata kotun shari’a
  • Alhaji Inuwa Uba ya ce Asiya-Balaraba Ganduje ta je gidansa ta dauke takardun filaye da kuma motoci
  • An samu sabani a kan nawa aka biya sadaki a lokacin auren ‘diyar Gwamnan, dole Alkali ya daga shari’a

Kano - Inuwa Uba wanda yake shari’a da Asiya-Balaraba Ganduje a wata kotun shari’a a jihar Kano ya zargi mai dakinsa da aukawa cikin gidansa.

Daily Nigerian ta ce Alhaji Inuwa Uba ya sanar da kotun shari’a mai zama a filin hoki cewa diyar Gwamnan Kano ta dauke wasu kaya daga inda yake zama.

A cewar Uba, da Asiya-Balaraba Ganduje ta fasa gidansa ta shiga, tayi gaba da wasu muhimman takardun filaye, abubuwan hawa irinsu motoci da mabudi.

Kara karanta wannan

Rikicin Cikin Gidan Jam’iyyar APC Yana Kara Fitowa Baro-Baro Daf da Zaben 2023

Wannan Bawan Allah ya sanar da kotun shari’ar da ke birnin Kano cewa mai dakinsa da ke neman Alkali ya raba su ta raba shi da wasu kayansa.

Takardun filaye a garuruwa

A rahoton da aka fitar, takardun da magidancin yake ikirari matarsa ta aure ta yi gaba da su, sun hada da takardar gidansa da ke Life Camp a Abuja.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

‘Diyar Gwamna Ganduje
Inuwa Uba da Balaraba Ganduje Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

Har ila yau akwai takardar C/O na wani gida da ke kusa da gidan gwamnati a Kano da makamancin takardar mallakar wurin taro na Amani duk a garin.

Sauran takardun sun kunshi na kamfanin ASIL Integrated Rice Mill a unguwar Gundutse da wasu takardu na filaye da ke garin Potiskum da Kano.

Asiya Ganduje ta tafi da motoci

Idan maganar ta tabbata, Hajiya Asiya Ganduje ta dauke Toyota Prado SUV ta 2017, Toyota Previa ta 2015 da Toyota Avensis 2019 daga gidan Inuwa Uba.

Kara karanta wannan

Assha: Dan takarar majalisa a jam'iyyar su Kwankwaso a Arewa ya sace N681m daga asusun banki

Sannan Lauyan wanda ake kara ya nuna ba N50, 000 aka biya a lokacin da aka auri wanda ta kai kara ba, ya bukaci a kara masa lokaci ya iya gano adadin.

Lauyan da yake kare diyar Gwamnan na jihar Kano, Ibrahim Nassarawa ya nuna bai san da labarin shiga gida ba, ya ce maganar ta fi karfin kotun shari’ar.

Alkali Abdullahi Halliru wanda yake sauraron shari’ar ya yi fatali da maganar Nassarawa. Sai zuwa ranar 19 ga watan Junairun nan za a koma kotu.

Shekaru 16 da suka wuce wadannan ma’aurata suka zama mata da miji, amma Asiya-Balaraba Ganduje ta nemi kotu ta tsinka igiyar dangantakarsu.

Dalilin kashe Ummita - Quangrong

An ji labari Frank Quangrong ya fadawa Alkali cewa ya kashe Ummukulsum Buhari ne a yunkurin ceton ransa da ya hango mutuwa a hannun Marigayiyar.

Mutumin Sin din da ake shari’a da shi ya ce a lokacin da ya ji labari bayan wasu ‘yan kwanaki cewa shi ya kashe Ummita, ya rusa kuka kan gangancin da ya yi.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Hadimar Gwamna Tambuwal Ta Mutu Sakamakon Cinkoso Lokacin Kamfen Atiku a Sokoto

Asali: Legit.ng

Online view pixel