Babban Malamin Addini Mai Karfin Fada A Ji A Najeriya Ya Yi Babban Rashi

Babban Malamin Addini Mai Karfin Fada A Ji A Najeriya Ya Yi Babban Rashi

  • Daya cikin shugabannin Cocin Redeemed Christian Church of God (RCCG), Farfesa Folagabade Aboaba, ya riga mu gidan gaskiya
  • Farfesa Aboaba wanda shine mataimakin shugaban shaharariyar cocin ya rasu ne a ranar Litinin, 23 ga watan Janairu bayan gajeruwar rashin lafiya
  • An rahoto cewa marigayi na daya daga cikin makusanta na shugaban cocin Fasto Enoch Adeboye

Mataimakin shugaban Cocin Redeemed Christian Church of God (RCCG), Farfesa Folagabade Aboaba, ya riga mu gidan gaskiya yana da shekaru 90.

Wani rahoto da The Punch ta wallafa ya ce Aboaba ya rasu ne a safiyar ranar Litinin, 23 ga watan Janairu, bayan gajeruwar rashin lafiya.

Adeboye da Aboaba
Babban Malamin Addini Mai Karfin Fada A Ji A Najeriya Ya Yi Babban Rashi. Hoto: PIUS UTOMI EKPEI/AFP (Getty Images), Twitter/@MobilePunch
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Legit.ng ta tattaro cewa marigayin na daya daga cikin makusantan shugaban cocin na RCCG, Fasto Enoch Adeboye.

Kara karanta wannan

2023: Tinubu Ya Gana Da Malaman Addini Na Arewa Maso Gabas, Ya Sha Alwashin Kamanta Adalci Da Gaskiya

Shugaban kungiyar injiniyoyin noma na kasa, Farfesa Folarin Alonge ne ya bayyana rasuwar mamacin cikin wata sanarwa da ya fitar.

Alonge ya jinjinawa Folagbade Aboaba

Alonge ya yi rubutu na jinjina ka marigayi Aboaba a shafin kungiyar, yana bayyana marigayin a matsayin daya cikin wadanda suka kafa kungiyar.

Ya ce marigayin mutum ne mai son cigaban aikin noma na zamani a Najeriya.

Alonge wrote:

"Daya daga cikin babban mu a aiki, Farfesa Fola Aboaba, ya tafi gida. Farfesa ne ya farfesoshi.
"Farfesa Folagbade Olajide Aboaba Farfesa Emeritus ne na Injiniyancin noma a Jami'ar Ibadan kuma shine Dean din sashin fasaha na farko daga (1976-1982). Ya koyar da ni a lokacin da na ke digiri na farko da na biyu. Jagora ne na mutane da dama da farfesoshi."

Alonge ya tuna haduwarsa na karshe da mataimakin shugaban na RCCG

A rubutun jinjinar, Farfesa Alonge ya ce sunyi hira da marigayin malamin a Satumban 2022.

Kara karanta wannan

Gwamna Kuma Farfesa Ya Bayyana Mutum Ɗaya Tilo da Zai Iya Ceto Najeriya a 2023

Ya rubuta:

"Na yi hira da shi a ranar 15 ga watan Satumba lokacin da muke shirin taron NIAE a Asaba (Jihar Delta). Amsar da ya bani da na tambayi lafiyarsa ya ce 'Na gode, ina tsufa amma lafiya. Mun gode Allah. Allah ya maka albarka. Baba mutum ne mai kirki, mai sakin fuska kuma mai halaye masu kyau."

Ya kara da cewa:

"Allah ya jikansa da rahama."

Hawaye da Alhini yayin da babban malamin addini ya mutu a Najeriya

A wani rahoton, Dakta Daniel Otoh, shugaban cocin The Shepherds House Assembly, fitaccen coci a Najeriya ya riga mu gidan gaskiya.

Kamar yadda Mrs Jackie Talena ta sanar da madadin cocin, ta ce Dr Otoh kwararren likita ne kuma ya rasu ne a ranar Lahadi 4 ga watan Disamba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel