Jam’iyyar APC ta Ambaci Jihar Arewa 1 da take Harin Karbe Mulkinta a Zaben 2023

Jam’iyyar APC ta Ambaci Jihar Arewa 1 da take Harin Karbe Mulkinta a Zaben 2023

  • Shugaban Jam’iyyar APC a Najeriya bai yafewa sauya-shekar da Gwamna Samuel Ortom ya yi zuwa PDP ba
  • Sanata Abdullahi Adamu ya ce ya wajaba APC ta kuma kafa Gwamnati a jihar Benuwai bayan zaben 2023
  • Mu’azu Bawa Rijau ya yi jawabi da yawun Adamu wajen kaddamar da yakin neman zaben APC a Benuwai

Abuja - Shugaban APC na kasa, Abdullahi Adamu ya tabbatarwa ‘ya ‘yan jam’iyya mai mulki cewa za su karbe iko da jihar Benuwai a zabe mai zuwa.

Daily Trust ta rahoto Sanata Abdullahi Adamu yana cewa kwace aka yi masu Benuwai inda gwamnan da mutane suka zaba a APC ya sauya-sheka.

Shugaban jam’iyyar ta APC a Najeriya ya yi kira ga shugabanninsa na reshen Benuwai da su dage wajen ganin mulki ya koma hannunsu a zaben Maris.

Kara karanta wannan

Jam’iyyar NNPP Ta Fasa Kwai, Wanda Aka ba Takara Ya Yaudare ta Bayan Karbar N500m

Adamu ya bukaci haka ne a lokacin kaddamar da yakin neman zaben ‘dan takaran Gwamnan APC zaben 2023 da aka yi wa take da: ‘Alialization Alia/Ode’.

APC ta soma kamfe a Gboko

APC mai adawa a Benuwai ta kaddamar da yakin neman zabenta ranar Laraba a garin Gboko.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Adamu ta bakin mataimakin shugaban jam’iyya na shiyyar Arewa maso tsakiya, Alhaji Mu’azu Bawa Rijau ya ce APC ta mutanen Benuwai ce.

Jam’iyyar APC
Yakin zaben APC Hoto: punchng.com
Asali: UGC

An rahoto Mu’azu Bawa Rijau yana cewa ba a raba Jam’iyyar APC da ‘yan jihar Benuwai musamman ganin nasarorin da gwamnatin Buhari ta samu.

Bayan shekaru kusan hudu, shugaban na APC yake cewa ya zama dole mulki ya koma hannunsu.

Tun 2018 ne jam’iyyar ta zama mai adawa a sakamakon sauya-shekar da Gwamna Samuel Ortom ya yi zuwa PDP – jam’iyyar da ya bari kafin zaben 2015.

Kara karanta wannan

Jagororin APC Sun Gaza Nunawa Tinubu Kara, Sun Kunyata Shi Wajen Yakin Zabe

Tikitin Musulmi da Musulmi a APC

A wajen, an ji Ministan harkoki na musamman, Sanata George Akume yana bayanin yadda ake yunkurin kawowa Bola Tinubu wajen zama shugaban kasa.

Tribune ta rahoto tsohon Gwamnan yana cewa duk masu bata tikitin Bola Tinubu da Kashim Shettima da sunan addini, ba za su kai labari a zaben bana ba.

Kanawa za su zabi Tinubu - Ganduje

An ji labari Abdullahi Umar Ganduje ya roki alfarmar Kanawa da su zabi Bola Tinubu da duka ‘Yan takaran da Jam’iyyar APC ta tsaida a zabe mai zuwa.

Gwamnan Kano ya kawo dalilan cancantar Tinubu, ya yi hasashen cewa zaben 2023 zai zo daidai da na 1993 inda MKO Abiola ya doke Alhaji Bashir Tofa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel