Shugaban Kungiyar Kafa Kasar Yarbawa Adeniran Ya Yi Murabus, Ya Bada Dalili

Shugaban Kungiyar Kafa Kasar Yarbawa Adeniran Ya Yi Murabus, Ya Bada Dalili

  • Zargin rashawa ya janyo rikicin shugabanci a kungiyar neman kafa kasar Yarbawa mai suna Ilana Omo Oodua Worldwide
  • Wale Adeniran, jagora kuma shugaban kungiyar, ya sanar da murabus dinsa domin bada daman a yi sahihin bincike kan zargin
  • Jagoran na kungiyar kafa kasar Yarbawa ya kallubalanci duk wani da ke da hujja a kansa ya taho ya nuna wa al'umma

Wale Adeniran, jagora kuma ciyaman din masu neman kafa kasar Yarbawa, wacce aka fi sani da Ilana Omo Oodua Worldwide, ya yi murabus daga matsayinsa a kungiyar kan zargin rashawa da almubarazanci.

Adeniran ya sanar da murabus dinsa a wani bidiyo da aka dora a shafin YouTube, mai suna Omoboriowo media, a ranar Asabar 7 ga watan Janairu.

Yoruba Nation
Shugaban Kungiyar Kafa Kasar Yarbawa Adeniran Ya Yi Murabus, Ya Bada Dalili. Hoto: Vuk Valcic/SOPA Images/LightRocket, Dave Rushen/SOPA Images/LightRocket
Asali: Getty Images

Jagoran na Yoruba Nation ya sauka daga mukaminsa ne domin ya bada dama a yi sahihin bincike kan zargin damfara da aka masa.

Kara karanta wannan

Hunturu: NiMet ta ce za a yi tsananin hazo na kwana 3, ta fadi jihohin da hakan zai shafa

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Adeniran ya kallubalanci duk wani da ke da hujja a kansa ko wani da ya tura wa kungiyar kudi ta hannunsa ya taho ya bayyana wa al'umma.

Ya yi kira ga shugabannin yarbawa su kafa kwamitin don bincikar zargin da ake masa.

Kalamansa:

"Ina son yin amfani da wannan damar don sanar da sauka na daga shugabancin Ilana Omo Oodua Worldwide, a matsayin mamba na Ilana Omo Oodua Worldwide, na sauka ne don bada damar a yi bincike kan zargin da ake min.
"Saboda a dukkan kasashen da suka cigaba, abin da suka saba yi shine idan an zargi mutum mai mukami, zai ajiye aiki don bada dama a yi bincike, abin da na yi kenan yanzu.
"Na gode muku, kuma duk abin da binciken ya haifar, za a sanar da al'umma. Bai kamata a boye ba. Za a bayyana sakamakon binciken don kowa ya san gaskiya kan zargin rashawa da damfara da ya shafi wannan gwagwarmayar namu. Nagode muku."

Kara karanta wannan

Yadda Matashi Ya Kera 'Motar Kara' Harda Sa Mata Injin, Ya Tashe Ta a Cikin Bidiyo

Gwamna Okeredolu ya ce kudu ne za ta mulki Najeriya shekaru takwas masu zuwa

A wani rahoto, gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, ya ce lokaci ya yi da yankin kudancin kasar ne za ta fitar da shugaban kasa na shekaru takwas masu zuwa.

Jigon na jam'iyyar All Progressives Congress, APC, ya ce ya zama dole a cigaba da gwagwarmayar ganin yankin kudu ta samar da shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel