Sarkin Bauchi Ya Kori Wazirinsa, Na Hannun Daman Atiku, Bello Kirfi, Kan Rashin Biyayya Ga Gwamnan Bauchi

Sarkin Bauchi Ya Kori Wazirinsa, Na Hannun Daman Atiku, Bello Kirfi, Kan Rashin Biyayya Ga Gwamnan Bauchi

  • Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya tube rawanin Wazirin Bauchi Alhaji Bello Kirfi
  • Masarautar jihar Bauchi ta sanar da sauke Alhaji Kirfi daga sarautar waziri kan zarginsa da 'rashin biyayya da girmama gwamnan' Bauchi
  • Bayan tube rawanin Kirfi, yarsa Sa'adatu Kabir Kirfi ta mika wasikar murabus daga mukaminta na Kwamishina a Bauchi

Bauchi - Masarautar Bauchi ta tube wa tsohon ministan ayyuka na musamman, Bello Kirfi, rawaninsa na 'Wazirin Bauchi' ta kuma cire shi daga majalisar sarakuna a karo na biyu cikin shekaru biyar.

Wannan sabon lamarin na da alaka da zargin da aka yi wa tsohon ministan na 'rashin girmamawa da biyayya' ga gwamnan jihar, Bala Mohammed, The Punch ta rahoto.

Bala Mohammed
Sarkin Bauchi Ya Kori Wazirinsa, Na Hannun Daman Atiku, Bello Kirfi, Kan Rashin Biyayya Ga Gwamnan Bauchi. Hoto: Daily Nigerian
Asali: UGC

Kirfi ya taba rasa rawaninsa a baya

Kirfi, tsohon ma'aikacin gwamnatin tarayya, ya rike minista a gwamnatin Alhaji Shehu Shagari a 1980s, kuma shine Pro Chancellor na Jami'ar Ilorin daga 1997-99.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yar Wazirin Bauchi Ta Yi Murabus Daga Mukaminta A Gwamnatin Bauchi Bayan Gwamna Ya Tsige Tube Rawanin Mahaifinta

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kuma zama ministan ayyuka na musamman a gwamnatin Olusegun Obasanjo a 2000s.

An sanar da cire dattijon ne cikin wata wasika da sakataren masarautar Bauchi, Alh Shehu Mudi Muhammad ya rattaba hannu a kai.

Tana dauke da kwanan wata na 3 ga watan Janairun 2023 da lamba BEC/ADM/20/VOL.XV

Muhammad, a cikin wasikar ya bayyana cewa Ma'aikatar Kananan Hukumomi na jihar ta sanar da majalisar sarakuna game da 'rashin girmamawa da biyayya' na Kirfi ke yi wa gwamna, don haka aka cire shi.

Ya ce:

"An umurci in duba wasika da aka samu daga Ma'aikatar Kananan Hukumomi mai lamba MLG/LG/S/72/T mai kwanan wata na 30 ga watan Disamban 2022.
"Abin da wasikar ta kunsa ta nuna rashin girmamawa da biyayyar ka ga mai girma gwamnan jiha. Don haka ta bukaci cire ka nan take.
"Don haka, an cire ka daga ofishin Wazirin Bauchi kuma mamba na majalisar sarakuna na Bauchi."

Kara karanta wannan

Sarkin Bauchi ya Tsige Mutumin Atiku daga Sarautar Waziri a Dalilin Rikici da Gwamna

A baya, masarautar ta Bauchi ta taba dakatar da Kirfi a Maris din 2017 a lokacin gwamna Mohammed Abubakar.

Hajiya Sa'adatu Kirfi ta yi murabus a matsayin kwamishina a Bauchi

A wani rahoton, kwamishinan gama kai da kananan masana'antu na jihar Bauchi, Hajiya Sa'adatu Bello Kirfi, ta yi murabus.

Ta yi murabus din ne jim kadan bayan da masarautar Bauchi ta tube rawanin mahaifinta a matsayin wazirin Bauchi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel