Sallar Layya: Gwamnati Ta Bada Hutun Kwanaki 7, Ta Kawo Dokokin Tsafta a Bangladesh
- Gwamnatin Firayim Minista Tarique Rahman ta ayyana hutun kwanaki bakwai na bikin babbar Sallah, wanda zai fara daga ranar 25 zga watan Mayu
- Tarique Rahman ne ya jagoranci taron majalisar zartarwa da aka gudanar a sakatariyar gwamnati inda aka amince da wannan hutun sallar na 2026
- Domin daidaita kwanakin aiki, an soke hutun ranar Asabar, 23 ga watan Mayu, inda dukkan ofisoshi za su kasance a buɗe kafin fara babban hutun
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Bangladesh - Gwamnatin Bangladesh ta sanar da hutun kwanaki bakwai na bikin Sallar Layya, wanda zai fara daga ranar 25 zuwa 31 ga watan Mayu.
An sanar da hakan ne bayan kammala taron Majalisar Zartarwa da aka gudanar a sakatariyar gwamnatin kasar a daren ranar 7 ga Mayu, ƙarƙashin jagorancin Firayim Minista Tarique Rahman.

Source: Getty Images
Bangladesh: An bada hutun babbar sallah
To sai dai, an soke hutun mako-mako na ranar Asabar, 23 ga watan Mayu, inda dukkan ofisoshi za su ci gaba da aiki kamar yadda jaridar The Business Standard ta ruwaito.
Wannan sanarwar ta fito ne ta hanyar wata wasiƙar da sashen gudanarwa na majalisar zartarwa ya fitar, in da ta bayyana cewa:
"Gwamnati ta ayyana hutun kwanaki bakwai daga 25 zuwa 31 ga watan Mayu domin bukukuwan babbar Sallah mai zuwa. Sai dai, za a bude ofisoshi a ranar 23 ga Mayu (Asabar) da 24 ga Mayu (Sunday)."
Baya ga batun hutu, taron majalisar ya amince da daftarin "Manufar tsaftar banɗakin jama'a ta kasa ta 2026."
Babban burin wannan tsari shi ne wayar da kan jama'a game da amfani, kiyayewa, da kuma tsaftar banɗakunan jama'a; tabbatar da samun ingantattun wuraren ba-haya cikin sauƙi a faɗin ƙasar domin inganta lafiyar al'umma ta fuskar tsafta; da kuma tabbatar da samar da wuraren da za su kasance masu sauƙin amfani ga mata, yara, nakasassu, tsofaffi, da kuma al'ummomin da aka maida saniyar ware.

Kara karanta wannan
Gwamnati za ta ba ma'aikata hutun kwanaki 9 domin bukukuwan sallar layya a Turkiyya
Shirin wayar da kan dalibai kan tsaftar bandaki
Wannan dabftarin zai tabbatar da ingantaccen tsarin gudanarwa da samar da kuɗaɗe domin dorewar amfanin banɗakunan jama'a na dogon lokaci.
Hakazalika, zai kafa hanyoyin sanya ido, tantancewa, da kuma sabunta manufofin a duk lokacin da buƙata ta taso, in ji rahoton Dhaka Tribune.
Ma'aikatar Ilimi, Ma'aikatar Lafiya, da sauran hukumomin yaɗa labarai za su haɗa gwiwa domin wayar da kan ɗalibai da sauran jama'a kan dabarun tsafta, kamar yadda rahoton ya nuna.

Source: Twitter
Tilasta gina 'ma'ajiyar kazanta' a Bangladesh
A wannan gabar, wajibi ne dukkan manyan ayyukan gine-gine da za a gudanar a kasar su haɗa da banɗakunan maza da na mata a wuri daban daban.
Haka kuma, an mayar da gina 'ma'ajiyar kazanta' a matsayin tilas ga dukkan banɗakuna, kuma ba za a yarda kazantar ta kwarara zuwa koguna, tafkuna, ko wasu magudanan ruwa ba domin kare gurbatar ruwa.
An ce ma'aikatar sufuri da sashin ƙananan hukumomi za su haɗa gwiwa don gina waɗannan banɗakuna a wuraren da suka dace a kan manyan hanyoyin ƙasa.
An bada hutun kwana 9 a Turkiyya
A wani labari, mun ruwaito cewa, Shugaba Recep Erdoğan ya ba da sanarwar ƙara hutun Sallar Layya na shekarar 2026 zuwa kwanaki tara ga ma'aikatan gwamnati a Turkiyya.
Bukukuwan sallar za su fada tsakanin 27 zuwa 30 ga watan Mayu, inda aka haɗe kwanakin aiki na Litinin da Talata don samun hutu mai tsawo.
Legit Hausa ta tattaro bayanai game da yadda ake gudanar da bukukuwan sallah a kasar Montenegro da wasu daga cikin garuruwan Turkiyya.
Asali: Legit.ng

