Harkar Kwayoyi: Abin da Abba Kyari Ya Fada da aka Koma Sauraron Shari’arsa da NDLEA

Harkar Kwayoyi: Abin da Abba Kyari Ya Fada da aka Koma Sauraron Shari’arsa da NDLEA

  • Nureni Jimoh SAN yana so kotu tayi watsi da karar da NDLEA ta shigar a kan DCP Abba Kyari
  • Lauyan da ya tsayawa ‘dan sandan ya ce babu dalilin zuwa kotu alhali ‘yan sanda suna bincike
  • Hukumar NDLEA tayi raddi, ta ce binciken ‘yan sanda ba zai hana ayi shari’a da su Kyari a kotu ba

Abuja - Tsohon shugaban dakarun IRT na ‘yan sanda watau DCP Abba Kyari ya kalubalanci ikon hukumar NDLEA na gurfanar da shi a kotu.

The Cable ta kawo rahoto a ranar Laraba, 18 ga watan Junairu 2023 cewa DCP Abba Kyari ya nemi kotu tayi fatali da zargin da NDLEA take yi masa.

Lauyan da ya tsayawa jami’in tsaron, Nureni Jimoh SAN ya gabatar da korafi cewa akwai nakasa tattare da zargin da hukumar NDLEA take yi a kotu.

Kara karanta wannan

Abba Kyari Ya Yi Mani Alkawarin N10m Domin Yi Wa Bukola Saraki Sharri – ‘Dan Fashi

Nureni Jimoh ya ce abin da ya kamata Lauyoyin NDLEA suyi shi ne, su jira ‘yan sanda su kammala binciken da suke yi, kafin su shigar da kara.

'Yan sanda suna binciken zargin - Lauya

An rahoto cewa wannan lauya ya sanar da kotun da ke sauraron karar cewa ‘yan sanda suna binciken DCP Kyari, kuma har an fitar da rahoton farko.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Bugu da kari, jami’in da ake zargi da hannu wajen harkar miyagun kwayoyi ya ce hukumar PSC tana da hurumin da za ta binciki duk wani ‘dan sanda.

Abba Kyari
DCP Abba Kyari a Kotu Hoto: www.bbc.com
Asali: UGC

Kamar yadda majalisar NJC za ta iya binciken ma’aikatan shari’a, Kyari ta hannun lauyansa ya ce dokar aikinsu ya ba PSC damar hukunta maras gaskiya.

A dalilin wadannan hujjoji, Vanguard ta ce Abba Kyari ya roki a soke karar da ke kan shi.

Kara karanta wannan

Doka a hannu: Kiristoci a jihar Arewa sun fusata, sun kone ofishin 'yan sanda saboda abu 1

Sauran wadanda ake tuhuma da laifi tare da mataimakin kwamishinan ‘yan sandan sun amince da wannan batu, suka roki ayi fatali da zargin da ake yi masu.

Doka ba ta hana shari'a da 'yan sanda ba - NDLEA

Babban jami’in shari’a na NDLEA, Sunday Joseph ya maida martani, ya na mai neman kotun ta ki sauraron rokon da lauyan wanda ake zargi ya gabatar.

Joseph ya ce lamarin ‘yan sanda ba kamar na sojoji ba ne, idan ana zarginsu da laifi, za a iya shari’a da su. Emeka Nwite ya dage karar zuwa 22 ga watan Maris.

Zargin yi wa Bukola Saraki kazafi

Kun samu rahoto Ayoade Akinnibosun da ake tuhuma da laifin fashi da makami a banki, ya ce Abba Kyari yi masa alkawarin kudi da bizar fita kasar waje

Akinnibosun ya fadawa kotu Kyari ne ya bukaci yayi wa Bukola Saraki kazafi, da farko ya turje, amma da barazana tayi yawa sai ya aikata abin da ake so.

Kara karanta wannan

Abokin Takarar Tinubu Ya Nuna Matsayarsa, Ya Gargadi Mutane a Kan ‘Dan Takaran APC

Asali: Legit.ng

Online view pixel