An Kama Amina Guguwa Yar Shekara 50 Kan Kashe Kishiyarta Yayin Dambe A Bauchi

An Kama Amina Guguwa Yar Shekara 50 Kan Kashe Kishiyarta Yayin Dambe A Bauchi

  • Jami'an yan sandan jihar Bauchi sun kama wata matar aure mai suna Amina Guguwa kan zarginta da kashe kishiyarta yayin dambe
  • Amina Guguwa yar shekara 50 ta halaka kishiyarta Amina Koli yar shekara 60 ne a ranar 1 ga watan Janairu kamar yadda rahoto ya bayyana
  • Yan sandan na Bauchi sun tura tawaga zuwa wurin da abin ya faru inda aka dauki gangan jikin Amina Koli zuwa asibiti kuma likitoci suka tabbatar ta rasu

Jihar Bauchi - Rundunar yan sandan jihar Bauchi ta bayyana cewa ta kama wata mata yar shekara 50 kan zargin kashe kishiyarta a Bauchi, rahoton The Punch.

Mai magana da yawun yan sandan jihar Bauchi, Ahmed Wakil, ne ya bayyana hakan cikin takardar da ya raba wa yan jarida a ranar Juma'a.

Kara karanta wannan

Hunturu: NiMet ta ce za a yi tsananin hazo na kwana 3, ta fadi jihohin da hakan zai shafa

Taswirar Bauchi
An Kama Amina Guguwa Yar Shekara 50 Kan Kashe Kishiyarta A Bauchi. Hoto: @MobilePunch.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce wacce ake zargin, Amina Guguwa, wacce ke zaune a kauyen Miya da ke karamar hukumar Warji, ta shake kishiyarta, Amina Koli, yar shekara 60, bayan dambe da suka yi a ranar 1 ga watan Janairun 2023.

Ya sanar da cewa:

"Amina Guguwa, wacce ake zargin, ta yi amfani da karfi ta shake wacce abin ya faru da ita sosai sakamakon hakan ta mutu nan take.
"Bayan samun rahoton, an tura tawagar yan sanda zuwa wurin da abin ya faru kuma suka dauke wacce abin ya faru da ita aka kai asibiti don bincike, inda likita ya tabbatar ta rasu."

A cewar shi, an fara bincike kan lamarin, sannan daga bisani za a gurfanar da wacce ake zargin a gaba kuliya don ta girbi abin da ta shuka, LIB ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yan Sanda Sun Dakile Harin Yan Ta'adda, Sun Sheke Daya, Sun Ceto Mutane A Katsina

Matan aure ta sheke mijinta domin ya ce zai karo mata abokiyar zama

A wani rahoton, Salamatu Shehu, wata matar aure da ke zane a Rafin Gero a karamar hukumar Anka a Zamfara ta sheke mijinta saboda ya ce zai mata kishiya.

Wani mazaunin kauyen, kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto ya ce wacce ake zargin ta yi wa mijinta rauni ne saboda fada mata cewa zai kara aure.

Rahotanni sun bayyana cewa Salamatu ta yi ajalin mijinta ne ta hanyar rantama masa kujera kuma nan take ya yanke jiki ya fadi summame, aka kai shi asibiti amma ya karasa a can.

Asali: Legit.ng

Online view pixel