Gwamna Ya Yi Garambawul a Majalisar Zartarwa da Kwamishinoni 2 Suka Ajiye Aiki
- Gwamna Sheriff Oborevwori ya yi garambawul a majalisar zartarwar jihar Delta sakamakon murabus ɗin wasu kwamishinoni biyu
- Kwamishinonin da suka yi murabus, Orode Uduaghan da ThankGod Trakiriowei, sun ɗauki matakin ne domin shiga takara a zaɓen 2027
- An umurci kwamishinonin harkokin mata da na gidaje su duba ayyukan ma'aikatun da aka bar gurabansu har zuwa nan da wani lokaci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Delta - Gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori, ya amince da wani ɗan karamin garambawul a majalisar zartarwarsa biyo bayan murabus ɗin wasu kwamishinoni biyu da ke neman muƙaman zaɓe gabanin babban zaɓen 2027.
Kwamishinan ayyuka (titunan karkara) da yaɗa labarai, Charles Aniagwu, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Juma'a a birnin Asaba.

Source: Twitter
Gwamna ya yi garambawul a Delta
Garambawul ɗin ya biyo bayan murabus ɗin kwamishinar ayyukan jinkai da ci gaban ƴaƴa mata, Orode Uduaghan, da kuma kwamishinan ci gaban matasa, ThankGod Trakiriowei.
Jaridar Punch ta ruwaito Aniagwu ya bayyana cewa:
“Sun yi murabus ne domin cimma burinsu na siyasa gabanin babban zaɓen 2027. Tsofaffin kwamishinonin sun sauka ne domin tsayawa takarar kujerun majalisar dokokin jihar Delta.”
Sakamakon wannan canji, an umurci kwamishinar harkokin mata da ci gaban al'umma, Pat Ajudua, da ta kula da ma'aikatar ayyukan jinkai da ci gaban ƴaƴa mata.
Haka kuma, kwamishinan gidaje, Godknows Angele, zai kula da ma'aikatar ci gaban matasa nan take.
Gwamna Sheriff Oborevwori ya gode wa tsofaffin kwamishinonin bisa ayyukan da suka yi wa jihar, sannan ya yi musu fatan alheri a harkar siyasar da suka sa gaba.
"Wannan canji dai zai ci gaba da aiki har sai lokacin da gwamnati ta ba da wani umarni na daban."
- Charles Aniagwu.
Sauran canje-canje a gwamnatin Oborevwori
Wannan ba shi ne karon farko da gwamnan yake yin canje-canje a majalisarsa ba a wannan shekarar, a cewar rahoton jaridar Vanguard.
Tun a watan Janairu, 2026 gwamnan ya amince da wani garambawul inda aka sauya wa wasu kwamishinonin wuraren aiki:
- Mista Michael Anoka ya tashi daga ma'aikatar tsare-tsare zuwa ma'aikatar makamashi.
- Mista Sunday Tataobuzogwu ya koma ma'aikatar tsare-tsare daga ta makamashi.
- Mrs. Rose Ezewu da Dr. Kingsley Ashibuogwu sun musanya gurabunsu a tsakanin ma'aikatun ilimin firamare da na sakandare.

Source: Original
Bugu da ƙari, gwamnan ya amince da naɗin Rt. Hon. Festus Ovie Agas, Rt. Hon. Frank Enekorogha, da Mista Charles Ajuyah (SAN) a matsayin mambobin majalisar gudanarwa ta jami'ar jihar Delta da ke Abraka.
Hadimin Oborevwori ya yanke jiki ya mutu
A wani labari, mun ruwaito cewa, an tabbatar da mutuwar babban mai tsara ayyukan gwamnan jihar Delta, Sunday Kotor bayan ya yanke jiki ya fadi a wurin taro.
Gwamna Sheriff Oborevwori ya yi alhinin rasuwar Sunday Kotor tare da mika sakon ta'aziyya ga iyalai da sauran 'yan uwansa.
Rahoto ya nuna cewa marigayin ya fadi ne a wani taro da ya shirya na kashin kasa, likitoci suka tabbatar da ya mutu bayan an garzaya asibiti.
Asali: Legit.ng

