Putin Ya Umurci A Tsagaita Wuta Na 'Wucin Gadi' A Yaki Da Ukraine, Ya Bada Dalili

Putin Ya Umurci A Tsagaita Wuta Na 'Wucin Gadi' A Yaki Da Ukraine, Ya Bada Dalili

  • Vladimir Putin, shugaban kasar Rasha ya bada umurnin a tsagaita wuta a yakin da kasarsa ke yi da Ukraine
  • Putin ya bada wannan umurnin ne saboda bawa mabiya addinin kiristanci na 'gargajiya' yin bikin kirsimeti a ranar 6 da 7 na watan Janairu
  • Shugaban na Rasha ya yi wannan kiran ne bayan da cocin kasar ta mika rokon alfarmar don mayakan su dawo yin addu'o'in kirsimeti

Rasha - Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin ya umurci ministan tsaro na kasar ya bada umurnin tsagaita wuta a yakin da ake da Ukraine saboda kirsimetin 'gargajiya'.

Za a fara tsagaita wutan ne cikin awa 36, za ta fara aiki daga ranar 6 ga watan Janairu, The Punch ta rahoto.

Vladimir Putin
Putin Ya Umurci A Tsagaita Wuta Na 'Wucin Gadi' A Yaki Da Ukraine, Ya Bada Dalili. Hoto: The Punch.
Asali: Facebook

Bikin Kirsimeti ta masu addinin kiristanci na gargajiya yasa aka tsagaita yakin Rasha da Ukraine

Kara karanta wannan

An tabo attajirai: Waya mafi tsada a duniya ta N21.5bn ta daina daukar WhatsApp

Bisa al'ada, mutane da dama na bikin kirsimetin 'gargajiyan' ne a ranakun 6 da 7 na watan Janairu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar kafar watsa labarai na Kremlin, Putin ya yi sanarwar ne bisa kiran da cocin Rasha ta yi a baya na neman a tsagaita wuta lokacin bikin.

Sanarwar da aka wallafa a shafin intanet na Kremlin ta ce:

"Saboda mabiya addinin kiristancin na gargajiya suna yankuna da dama da ake rikici, muna kira ga bangaren Ukraine ta tsagaita wuta ta bari su halarci addu'o'in jajiberi da ranar kirsimeti."

Cocin na Kirill na cikin masu goyon bayan matakin da gwamnatin Rasha ke dauka kan Ukraine - har tana fada wa sojojin Rasha cewa idan suka mutu wurin yakin, za a 'wanke dukkan zunubansu'.

Shugaban Turkiyya ya roki Putin ya kawo karshen yakin kasarsa da Ukraine

A baya, a ranar Alhamis, Shugaban kasar Turkiyya, Tayyip Erdogan ya yi kira ga shugaban na Rasha ya tsagaita wuta domin bada damar kawo karshen yakin.

Kara karanta wannan

Daga Shigowa Shekarar 2023, Kamfonin Lantarki Sun Yi Karin Farashin Wuta a Boye

A martaninsa, Putin ya nanata cewa Ukraine ta amince da karbe wasu yankunan Ukraine hudu da Moscow ta yi kafin a fara maganar kawo karshen yakin.

Mutane da kungiyoyi da dama sun soki kwace yankunan na Ukraine da Rasha ta yi da aka ce 'ya saba wa doka' amma hakan bai sa Rasha ta janye ba.

Dan Zambiya da ta tafi taya Rasha yaki da Ukraine ya mutu

A wani labarin, kun ji cewa Lemekhani Nathan Nyirenda, dan kasar Zambiya da ya tafi taya Rasha yaki da Ukraine ya rasu.

An dawo da gawarsa kasarsa ta Zambiya a jirgin sama inda aka sauke ta a fillin jiragen sama na Kenneth Kaunada, a cewar majiya daga danginsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel