Yadda Sojojin Isra'ila ke ba Iran Bayanan Sirri Ta Bayan Fage
- Rahotanni sun nuna cewa ‘yan sandan Israel sun kama sojoji uku da wani farar hula bisa zargin yi wa jami’an leken asirin Iran aiki tsawon shekaru
- Wasu bayanai sun nuna cewa mutane huɗun sun kasance suna hulɗa na dogon lokaci da jami’an leken asirin Iran da Isra'ila ke nuna adawa da ita
- An sanar da cewa ana zargin sun dauki hotunan wurare daban-daban a faɗin Isra’ila, ciki har da makarantar rundunar sojin saman Isra’ila
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Isra'ila - An gurfanar da wani farar hula da sojojin Isra'ila uku a ranar Juma’a bayan an kama su bisa zargin kasancewa suna hulɗa ta dogon lokaci da jami’an leƙen asirin Iran.
An zarge su da aiwatar da ayyukan tsaro ta bayan fage kafin shiga aikin soja, kamar yadda ‘yan sandan Isra’ila da rundunar binciken laifuffukan soja suka tabbatar a wata sanarwa.

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun nuna rashin imani, sun bude wa mutane wuta a wurin jana'iza a Filato

Source: Getty Images
Roya News ta ce an gurfanar da mutanen ne a daidai lokacin da Isra'ila da Iran ke zaman doya da manja bayan yakin kwana 40 da suka yi.
Sojojin Isra'ila da aka kama
Rahoto ya ce an kama sojojin ne a wani samame na haɗin gwiwa tsakanin jami'an 'yan sanda da sashen binciken laifuffukan soja.
Binciken ya gano cewa ana zargin ɗaya daga cikin waɗanda ake tuhumar ne ya jawo sauran tare da ba su umarnin gudanar da ayyukan ɗaukar hotuna a faɗin ƙasar.
Alakar sojojin Isra'ila da Iran
Hukumomin kasar Isra'ila sun ce an kuma nemi waɗanda ake tuhumar da su sayo makamai kuma waɗanda ake zargi sun aika hotunan wuraren taruwar jama’a da makarantar fasaha ta rundunar sojin sama
A matsayin wani ɓangare na ayyukan da ake zargin an ba su, waɗanda ake tuhumar sun tattara tare da aika hotuna da bidiyon tashoshin jirgin ƙasa, cibiyoyin kasuwanci, kyamarorin tsaro da sauran wurare.
Jerussalem Post ta wallafa cewa ana kuma zargin sun aika hotunan makarantar fasaha ta rundunar sojin saman Isra’ila, inda wasu daga cikinsu suka yi karatu.

Source: Getty Images
An ce lamarin ya ƙara nuna ƙoƙarin Iran na ɗaukar mutane aiki a cikin Isra’ila, ciki har da lamuran da suka shafi sojoji da fararen hula da ake zargi da tattara bayanan sirri ko aiwatar da ayyuka domin jami’an Tehran.
Poland ta caccaki Isra'ila
A wani labarin, mun kawo muku cewa gwamnatin kasar Poland ta gargadi jami'an Isra'ila kan yadda sojojinta suke wulakanta addini a Lebanon da wasu yankuna.
Hakan na zuwa ne bayan wani sojan kasar Isra'ila ya sanya wa mutum mutumin mamar Yesu Almasihu sigari a baki a wani kauyen Kiristoci a kasar Lebanon.
Ministan harkoki wajen Poland ya bayyana cewa akwai bukatar yi wa sojojin Isra'ila horo na musamman kan yadda suke cin zarafin mutane da addinai.
Asali: Legit.ng
