Matar Abiola Ta Kai Karar Shugaban ‘Yan Sanda, Tana Neman Naira Biliyan 100 a Kotu
- Farfesa Zainab-Duke Abiola ta na so kotu ta umarci jami’an ‘yan sanda su biya ta Naira Biliyan 100
- Matar MKO Abiola tana neman diyyar N100bn saboda zargin bata mata suna da ‘yan sanda suka yi
- Zainab-Duke Abiola ta ce an bata mata suna ta hanyar hada-kai da dogarinta, wajen shirya kazafi
Abuja - Farfesa Zainab-Duke Abiola, daya daga cikin matan Marigayi Cif MKO Abiola, ta shigar da karar shugaban ‘yan sandan Najeriya a wata kotun tarayya.
A rahoton da Vanguard ta fitar, an fahimci cewa Farfesa Zainab-Duke Abiola tana karar Sufetan ‘yan sandan da wasu mutane hudu a kotun tarayya a Abuja.
Mai karar tana tuhumar yaron Sufetan ‘yan sanda, Ibrahim Alkali da Teju Moses wanda ya yi aiki a matsayin babban 'dan sandan da ke aikin ba ta tsaro.

Kara karanta wannan
Asiri Ya Tonu: An Kama Wani Mai Hannu a Harin Jirgin Kasan Kaduna-Abuja, An Gano Abu 3
Zainab-Duke Abiola ta fadawa kotu wadannan mutane sun hada-kai da Teju Moses a lokacin shi ne dogarinta, sun yi mata sharrin cin zarafin Ibrahim Alkali.
Ba ayi mani adalci ba - Zainab-Duke Abiola
Farfesa Abiola tayi tir da ‘yan sanda na kin binciken lamarin da kyau, sai kurum suka gabatar da ita a gaban manema labarai a matsayin wanda tayi laifi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A watan Satumban 2022, jami’an tsaro suka gabatar da mai dakin Marigayin da sunan gwabje wani. Abiola ta ce zargin da ake yi mata, ba gaskiya ba ne.

Asali: UGC
Kamar yadda rahoto ya zo daga gidan talabijin Channels, Tawo Tawo ne Lauyan da ya shigar da kara mai lamba FHA/ABJ/CS/2370/202 a madadin Farfesan.
Tawo Tawo (SAN) yake cewa zargin da ake jefi Duke Abiola ya bata mata suna da mutunci, a dalilin haka ta bukaci Alkali ya bada umarni a biya ta N100m.
“Wannan lamari ya jawo mani matsala, tashin hankali da rashin lafiya, kuma ya bata sunana da mutuncina a Duniya, duk da irin matsayin da na kai a Duniya.
Shi Ibrahim Alkali ya hada-kai da tsohon dogari na, ya yi karyar na ci masa zarafi. Idan an je kotu, mu na da kyamarar CCTV da zai nuna abin da ya faru.”
- Farfesa Zainab-Duke Abiola
Nan da ranar 28 ga watan Fubrairun 2023, Alkali zai zartar da hukunci a kotun mai zama a Abuja.
Farashin man fetur
Ku na da labari Gwamnati ta ce babu maganar karin farashi a Najeriya duk da wahalar fetur ya karu sosai, musamman a 'yan kwanakin bayan nan.
Shugaba Muhammadu Buhari bai amince da karin kudin fetur a lokacin nan da ake cikin wahala ba., Ministan fetur yace Buhari ya damu da halin talaka.
Asali: Legit.ng