Manyan Labarai A Yau
Wasu jami'an tsaro na Civilian Joint Task Force (CJTF) sun rasa rayukansu bayan 'yan ta'addan ISWAP sun dasa musu bam a jihar Borno. Wasu sun samu raunuka.
Wata mai yin sharhi, Titilope Anifowoshe ta yi hasashen cewa nan da watan Yunin 2024, farashin man fetur zai ragu zuwa tsakanin N570-N580 kan kowace lita.
Faston da ya yi hasashen duniya za ta tashi a ranar 25 ga watan Afirilun 2024, ya fito ya fadi dalilin da ya sanya hasashen nasa bai tabbata ba. Ya ce addu'a ya yi.
Kamfanin mai na MRS Oil Plc ya sanar da rage farashin man dizal a dukkanin gidajen mai mallakinsa a fadin Najeriya biyo bayan rage farashi da matatar Dangote ta yi.
Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, ta caccaki tsohon gwamnan jihar Kogi kan kin mika kansa ga hukumar EFCC domin a bincike shi.
Wata matar aure mai dauke da juna biyu ta haihu a cikin daji a hannun masu garkuwa da mutane bayan sun sace ta a jihar Enugu. Ta haifi jariri namiji.
Dakarun rundunar sojojin Najeriya sun samu nasarar hallaka wasu 'yan ta'adda guda bakwai a yayin wani artabu da suka yi a jihar Sokoto. Sun kwato makamai.
Kakakin majalisar wakilai, Abbas Tajudeen, ya bayyana cewa Najeriya tana asara mai tarin yawa sakamakon gangar danyen man fetur 300,000 da ake sacewa a kullum.
Kwanaki bayan Naira ta yi tashi har ana murna, yanzu Dala ta koma sukuwa a kan kudin Najeriya. A baya kaya sun fara rage tsada a kasuwa, yanzu lamarin zai canza.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari