Dalilin da Ya Sanya Duniya Ba Ta Tashi a Ranar 25 Ga Afirilu Ba, Fasto Ya Yi Bayani

Dalilin da Ya Sanya Duniya Ba Ta Tashi a Ranar 25 Ga Afirilu Ba, Fasto Ya Yi Bayani

  • Wani mai wa'azi a Najeriya, Fasto Metuh ya ce duniya ba ta ƙare ba ne a ranar Alhamis, 25 ga watan Afirilu saboda shi da mambobinsa sun yi azumin kwanaki 21 da addu'o'i
  • Fasto Metuh ya ce ubangiji ya amsa adduo'insu, ya nuna jinƙansa ga duniya sannan ya ba mutanen duniya ƙarin lokaci domin su ƙara rayuwa
  • Ƴan Najeriya sun garzaya shafinsa na kafar sada zumunta domin bayyana ra'ayoyinsu bayan hasashensa bai tabbata ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Wani Fasto mai da'awar wa’azi, Fasto Metuh, wanda ya bayyana cewa duniya za ta ƙare a ranar Alhamis, 25 ga watan Afrilu, ya bayyana dalilin da ya sa hasashen nasa bai tabbata ba.

Fasto Metuh, ya bayyana dalilin nasa ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa X (wanda a baya aka fi sani da Twitter).

Kara karanta wannan

Buhari ya yi ta'aziyya yayin da tsohon sanata da ɗan uwan tsohon hadiminsa suka rasu a Kano

Fasto ya fadi dalilin rashin tashin duniya
Fasto Metuh ya ce ubangiji ya kara mana aron lokaci Hoto: @prophetmetuh
Asali: Twitter

Faston ya ce hasashen nasa bai tabbata ba ne saboda shi da mambobinsa sun yi azumi da addu'o'i na kwanaki 21.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamansa:

“Ubangiji ya nuna mana jinƙai. Bayan azumi da addu'o'inmu na kwanaki 21, ya ji mu kuma ya ba mu lokaci domin mu rayu. Addu'a tana aiki #rapture2024 #rapture."

Ƴan Najeriya sun yi martani

@Pedwardx ya rubuta:

"Ni rashin kunyar ce ma ta ba ni mamaki. Ka tuba kawai."

@yesscoco ya rubuta:

“To sauran kwana nawa ubangiji ya ba mu?"

@abeeb_azeez ya rubuta:

"Alagba Metu ba za ku huta ba."

@Adesoji85832525 ya rubuta:

"Yallabai, kawai ka ce kana son fara sana'ar barkwanci, za mu fi fahimta da kyau."

@AbiodunOmonijo ya rubuta:

"Dama kana cikin yin azumin kwanaki 21 da addu'o'i lokacin da ka yi sanarwar, meyasa ka yi tunanin cewa hakan zai faru? Ka yi tunani mai kyau kuwa?

Kara karanta wannan

Malam El-Rufai zai kara da Tinubu a zaben shugaban ƙasa a 2027? Gaskiya ta bayyana

@___McNairMill ya rubuta:

"Ka dai na amfani da Kiristanci domin neman suna."

Shekarar da duniya za ta tashi

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani Bature wanda yake a ƙasar Amurka ya ce nan da shekarar 2028 za a yi tashin duniya.

Mutumin mai suna Leslie Southam wanda yake da shekara 53 a lokacin da ya yi wannan hasashen a shekarar 2021, ya ce zai killace kansa a waje ɗaya har a yi tashin duniya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel