Bam Ya Hallaka Jami'an CJTF 5 a Jihar Borno, Wasu Sun Samu Raunuka

Bam Ya Hallaka Jami'an CJTF 5 a Jihar Borno, Wasu Sun Samu Raunuka

  • Wani bam da ƴan ta'addan ISWAP suka dasa a kan hanya ya yi sanadiyyar salwantar da rayukan aƙalla jami'an tsaro CJTF guda biyar a jihar Borno
  • Jami'an suna kan hanyarsu ta zuwa aikin sintiri ne lokacin da motarsu ta taka bam din bisa kuskure a kusa da ƙauyen Gajibo
  • Wasu daga cikin jami'an da harin ya ritsa da su sun samu raunuka inda aka garzaya da su zuwa asibiti domin ba su kulawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Aƙalla jami’an Civilian Joint Task Force (CJTF) biyar ne suka rasa ransu a jihar Borno.

Jami'an na CJTF sun rasa ransu ne bayan sun taka wani bam da ƴan ta’addan ISWAP suka binne a ƙaramar hukumar Dikwa ta jihar Borno.

Kara karanta wannan

Rundunar sojojin sama ta ragargaji 'yan ta'adda a jihar Neja

Bam ya kashe jami'an CJTF a Borno
Jami'an CJTF sun rasu a wani harin bam a Borno Hoto: @govborno
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa lamarin ya auku ne a kusa da ƙauyen Gajibo da misalin ƙarfe 12:30 na rana a ranar Asabar, 27 ga watan Afirilun 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda lamarin ya auku

Jami'an tsaron dai sun rasu nan take lokacin da suka taka bam ɗin wanda ƴan ta'addan suka binne lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa aikin sintiri.

Wani majiyar tsaro ya bayyana cewa:

"An dasa bam a wajen ƙauyen Gajibo cikin ƙaramar hukumar Dikwa wanda ya hallaka aƙalla jami'an CJTF guda biyar, yayin da wasu suka samu munanan raunuka."

Wani babban kwamandan CJTF a Maiduguri ya tabbatar da aukuwar harin, inda ya ƙara da cewa jami'an suna kan hanyar aikin sintiri ne lokacin da suka taka bam ɗin bisa kuskure a kusa da ƙauyen Gajibo a ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Yahaya Bello: Lauya ya hango kuskuren hukumar EFCC, ya yi gargadi

Ya ce wasu mambobinsu sun rasu amma bai bayyana adadinsu ba.

Mutum nawa bam ya raunata?

Zagazola Makama wani masani kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi ya ce majiyoyi sun bayyana cewa wasu mutum uku da abin ya shafa sun samu raunuka daban-daban.

Waɗanda suka samu raunuka a cewar majiyoyin an kwashe su zuwa asibiti, yayin da jami'an CJTF takwas da suka rasu aka kai su ga iyalansu domin yi musu jana'iza.

Legit Hausa ta tuntuɓi Malam Aliyu, wani mazaunin jihar Borno wanda ya nuna alhininsa kan wannan kisan da ƴan ta'addan suka yi wa jami'an tsaron.

Ya bayyana cewa rashin da aka yi na su babbar asara ce duba da yadda suka sadaukar da rayukansu wajen ganin an samu tsaro a jihar.

A kalamansa:

"Eh gaskiya wannan babban rashi ne duba da yadda suka sadaukar da kansu wajen ganin an samu tsaro a jihar nan. Kisan na su asara ce mai girma."

Kara karanta wannan

Sojoji sun sheke 'yan ta'adda 7 a wani sabon artabu a Sokoto

"Muna kira ga gwamnati duk da dama tana yin ƙoƙarinta idan irin hakan ya faru, da ta duba iyalan da suka bari domin rage musu raɗaɗin zafin wannan rashin da suka yi."

An kashe ƴan ta'adda a Borno

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya da aka tura domin yaki da ta'addanci a yankin Arewa maso Gabas sun kashe ƴan ta'adda biyu a jihar Borno.

Dakarun sojojin sun samu nasarar kashe ƴan ta'addan ne yayin da suke kan hanyar zuwa kai farmaki a kauyen Mashurori.

Asali: Legit.ng

Online view pixel