Yadda Matar Aure Mai Ciki Ta Haihu a Hannun Masu Garkuwa da Mutane Cikin Daji

Yadda Matar Aure Mai Ciki Ta Haihu a Hannun Masu Garkuwa da Mutane Cikin Daji

  • Wata matar aure da masu garkuwa da mutane suka sace a jihar Enugu tana ɗsuke da juna biyu ta haifi jariri namiji a cikin daji
  • Mijin matar wanda ya tabbatar da hakan ya bayyana cewa sai da ya biya kuɗin fansa N1.6m kafin miyagun su sako matar da jaririn da ta haifa
  • Tsautsayi dai ya faɗa kan matar ne bayan masu garkuwa da mutanen sun sace ta lokacin da take kan hanyar zuwa asibiti tare da ƴaƴanta guda biyu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Enugu - Wata mata mai juna biyu da aka yi garkuwa da ita ta haihu a hannun masu garkuwa da mutane a ƙaramar hukumar Udi ta jihar Enugu.

Kara karanta wannan

Kaduna: Farashin litar fetur ya haura N1,000 yayin da aka fara dogon layi a gidajen mai

Matar dai an yi garkuwa da ita ne yayin da take kan hanyarta ta zuwa asibiti domin haihuwa a yankin Egede, na ƙaramar hukumar Udi.

Matar ta haihu a hannun masu garkuwa da mutane
Matar aure ta haihu cikin daji a hannun masu garkuwa da mutane Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Lamarin wanda ya auku a ranar Litinin ɗin da ta gabata, ya sanya matar ta haifi jariri namiji a cikin daji, cewar rahoton jaridar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An tattaro cewa matar mai suna Chinwendu Igwe, tana tare da wasu ƙananan ƴaƴanta guda biyu masu shekaru tsakanin huɗu zuwa biyu a lokacin da lamarin ya faru.

Yadda lamarin ya auku

Mijin matar, Mista Ekene Igwe, wanda ya tabbatar wa manema labarai haka ya ƙara da cewa ya biya kuɗin fansa N1.6m kafin a sako matarsa ​​da yaronsa daga dajin Egede inda masu garkuwa da mutane suka nemi ya ajiye kuɗin fansan.

Ekene Igwe ya ce wani mai babur ne ya ceci yaransa biyu da masu garkuwa da mutane suka yi watsi da su a kan hanya, rahoton Daily Post ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An kama matashin da ya haɗa baki da wasu suka yi barazanar sace kawunsa

A kalamansa:

"Na biya kudin fansa Naira miliyan 1.6 kafin in samu matata da sabon jaririn."

Igwe wanda ya fito daga garin Attakwu Akegbe Ugwu Awkunanaw ya ce yana godiya ga Allah da ya dawo masa da matarsa ​​gida lafiya.

Da yake tsokaci kan lamarin mai gidan da Ikene yake yin haya, Cif Emma Ugwu, Enyiduru, ya ce matar da aka ceto yanzu haka tana asibitin Parklane da ke Enugu inda gwamnan jihar Enugu ke kula da lafiyarsu.

Ɗaliban jami'a sun kuɓuta

A wani labarin kuma, kun ji cewa ragowar daliban jami’ar tarayya da ke Gusau, Jihar Zamfara da aka sace a ranar 22 ga Satumba, 2023, sun kuɓuta daga hannun ƴan bindiga.

An sako ɗaliban ne su 23 a Kuncin Kalgo da ke ƙaramar hukumar Tsafe a jihar Zamfara kuma aka mika su ga jami’an gwamnati.

Asali: Legit.ng

Online view pixel