Kasar Iran Ta Gabatar da Sakon Farko ga Tawagar Pakistan kan Batun Sulhu da Amurka
- Gwamnatin Iran ta mika sakon godiya ga Pakistan bisa yadda ta yi ruwa ta yi tsaki a kokarin sulhunta kasar da Amurka
- Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi ne ya bayyana hakan bayan ya karbi tawagar Pakistan da ta kai ziyara Tehran yau Laraba
- Rahotanni sun nuna cewa jami'an Iran sun shiga ganawa da tawagar Pakistan kuma ana sa ran za a yi maganar komawa tattaunawa da Amurka
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Iran - Gwamnatin kasar Iran ta godewa Pakistan bisa rawar da take takawa wajen ganin an yi sasanci tsakaninta da Amurka domin samun zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya.
Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ne ya mika wannan sakon godiya jim kadan bayan ya karbi tawagar Pakistan a filin jirgin sama na birnin Tehran yau Laraba.

Source: Getty Images
Dalilin Pakistan na tura tawaga Iran
Tashar LAl-Jazeera ta ruwaito cewa tawagar Pakistan ta kai ziyara kasar Iran ne domin isar da sakon Amurka da kuma duba yiwuwar sake komWa teburin tattaunawa tsakanin kasashen biyu
Babban hafsan sojin kasar Pakistan, Asim Munir ne ya jagoranci wannan tawaga ta musamman da ta kai ziyara kasar Musulunci ta Iran.
Iran ta mika godiya ga kasar Pakistan
Da yake isar da sakon farko bayan tarbar tawagar Janar Munir, Ministan Harkokin Wajen Iran ya ce Pakistan ta dage wajen ganin an masalaha tsakanin Amirka da Iran.
Rahotanni sun nuna cewa Abbas Araghchi ya godewa Pakistan ne a jawabin da ya yi bayan shiga ganawa da tawagar kasar, wanda bayanai suka nuna har yanzu ba su fito daga zaman ba.
Araghchi ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, inda ya ce ya nuna “godiya ga kyakkyawan tarɓar baƙi da Pakistan ta yi a lokacin tattaunawar,” da aka yi a birnin Islamabad.
Iran da Pakistan na da alaka mai karfi
Ministan ya ƙara da cewa hakan yana nuna ƙaƙƙarfar dangantaka mai zurfi da ke tsakanin ƙasashen biyu.
Ya jaddada cewa haɗin gwiwar Iran da Pakistan wajen inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin na nan daram kuma suna tafiya tare.

Source: Getty Images
“Ƙudirin mu na inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin Gabas ta Tsakiya yana nan daram kuma muna aiki tare a kai,” in ji shi.
Araghchi ya kuma wallafa bidiyo inda aka gan shi yana rungumar Janar Munir a filin jirgin sama yayin isowarsa, abin da ke nuna kyakkyawar alaƙa da fahimtar juna tsakanin ɓangarorin biyu.
Mutanen Iran ba za su taba mika wuya ba
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa duk wuya duk runtsu, Iraniyawa ba za su taba mika wuya ga wata kasa ba a duniya.
Shugaba Pezeshkian ya bayyana cewa hare-haren da Amurka da Isra'ila suka kaddamar kan Iran sun saba wa dokokin kasa da kasa na duniya.
Ya soki salon manufofin manyan ƙasashen duniya na yanzu, yana mai jaddada cewa duk wani harin soja da aka kai wa ƙasashe masu cin gashin kansu, ya sabawa ka'idojin da aka amince da su.
Asali: Legit.ng

