Iran da Amurka Za Su Sake Zama don Kawo Karshen Yaki

Iran da Amurka Za Su Sake Zama don Kawo Karshen Yaki

  • Tawagogin Amurka da Iran sun kasa cimma yarjejeniya a zaman farko da suka yi domin kawo karshen yakin da ake yi a Gabas ta Tsakiya
  • Majiyoyi sun bayyana cewa za a sake zama domin gudanar da zagaye na biyu na tattaunawar a birnin Islamabad na kasar Pakistan
  • Tuni dai aka sanar da bangarorin biyu kan bukatar su sake zama domin ci gaba da tattaunawar da aka fara

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Islamabad, Pakistan - Akwai yiwuwar tawagogin tattaunawa daga Amurka da Iran su koma ƙasar Pakistan a ƙarshen wannan mako.

Tawagogin za su koma ne domin ci gaba da tattaunawa kan kawo ƙarshen yaƙi a yankin Gabas ta Tsakiya.

Amurka da Iran na iya sake zaman tattaunawa
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump da shugaban majalisar dokokin Iran, Mohammad Bagher Ghalibaf Hoto: Nurphoto
Source: Getty Images

Tashar Reuters ta ce jami’an Pakistan da na Iran suka bayyana mata hakan a ranar Talata, 14 ga watan Afirilun 2026.

Kara karanta wannan

Babbar bukatar da Amurka ta gabatarwa Iran yayin tattaunawa a Pakistan

Amurka da Iran za su sake zama

Hakan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan da tattaunawar farko ta ƙare ba tare da an cimma wata matsaya ba.

Har yanzu dai babu wani tabbaci daga jami’an Amurka game da wannan shiri, wanda jami’an Iran da na Pakistan suka tattauna a matsayin sirri ba tare da an bayyana sunayensu ba.

Wata majiya da ke da masaniya kan tattaunawar ta ce an riga an aika wa Washington da Tehran wata shawara na cewa tawagogin su koma Islamabad domin ci gaba da tattaunawa.

Yaushe za a sake zama?

Ko da yake ba a tsayar da takamaiman rana ba, ƙasashen biyu na iya komawa tattaunawar tun a ƙarshen wannan mako.

Wani jami’i a ofishin jakadancin Iran da ke Islamabad ya ce:

“Za a iya gudanar da zagaye na gaba na tattaunawar a ƙarshen wannan mako ko kuma farkon mako mai zuwa. Amma kawo yanzu ba a kammala komai ba.”

Kara karanta wannan

Iran ta fadi babban abin da ya hana samun daidaito tsakanin kasar da Amurka

Tun da fari, wata babbar majiya daga Iran ta bayyana cewa:

"Ba a sanya takamaiman rana ba, amma tawagogin sun ware ranar Juma’a zuwa Lahadi a matsayin ranakun da za su iya zama.”

Haka zalika, wani babban jami’in Pakistan ya ce Islamabad ta tuntuɓi Iran “kuma mun samu amsa mai kyau cewa a shirye suke su halarci zagaye na biyu na tattaunawar.”

Tawagar Iran za ta iya sake zama da ta Amurka
Tawagar Iran yayin da ta isa birnin Islamabad don tattaunawa da Amurka Hoto: @visegrad
Source: Twitter

Ba a ji ta bakin Amurka da Pakistan ba

Wannan taro na ƙarshen makon da ya gabata shi ne karon farko da jami’an Amurka da na Iran suka fuskanci juna kai-tsaye cikin fiye da shekara 10 kuma shi ne tattaunawa mafi girma tsakanin ƙasashen biyu tun bayan Juyin Juya Halin Musulunci na 1979 a Iran.

Kawo yanzu, ma’aikatar wajen Pakistan, rundunar sojoji, da ofishin firaminista ba su ba da amsa ba kan buƙatar jin ta bakinsu dangane da lamarin.

Fadar White House ma ba ta ba da martani nan take ba.

Donald Trump ya yi barazana ga Iran

Kara karanta wannan

Netanyahu ya yi fatali da zaman sulhu da ake yi, ya sake shan alwashi kan Iran

A wani labarin kuma, kun ji cewa Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya sake yin barazana ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Trump ya yi barazanar lalata duk wani jirgin ruwan yakin Iran da ya tunkari shingen da dakarun sojojin Amurka suka kafa kan tashoshin jiragen ruwan kasar.

Barazanarsa na zuwa ne duk da kiraye-kirayen da ƙasashen duniya ke yi na a girmama yarjejeniyar tsagaita wuta tare da komawa teburin tattaunawa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng