Rundunar Sojojin Sama Ta Ragargaji 'Yan Ta'adda a Jihar Neja

Rundunar Sojojin Sama Ta Ragargaji 'Yan Ta'adda a Jihar Neja

  • Rundunar sojojin saman Najeriya (NAF) ta kai hare-hare ta sama kan maɓoƴar ƴan ta'addan da suka addabi mutane a jihar Neja
  • Haren-haren sun hallaka ƴan ta'adda masu tarin yawa tare da lalata maɓoyarsu da ke cikin dajin yankin Allawa na ƙaramar hukumar Shiroro
  • Ƴan ta'addan su ne ke da alhaki kan harin da aka kai wa sojoji wanda ya yi sanadiyyar rasa mutum shida daga cikinsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Rundunar sojojin saman Najeriya (NAF) ta yi nasarar hallaka ƴan ta'adda tare da lalata maɓoyarsu a jihar Neja.

Ƴan ta'addan dai sune suka kai hari tare da kashe sojoji shida a ƙaramar hukumar Shiroro ta jihar Neja.

Kara karanta wannan

Bam ya hallaka jami'an CJTF 5 a jihar Borno, wasu sun samu raunuka

Sojojin sama sun hallaka 'yan ta'adda
Hare-haren sojojin sama sun hallaka 'yan ta'adda a Neja Hoto: Nigeria Air Force
Asali: Facebook

Hakan na ƙunshe ne a cikin sanarwar da daraktan hulɗa da jama’a da yaɗa labarai na NAF, Air Vice Marshal Edward Gabkwet ya fitar a ranar Lahadi, cewar rahoton jaridar Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce an kai harin ne a ranar 27 ga wafan Afrilu, 2024, bayan bayanan sirri sun nuna tarin bukkoki da ƴan ta’addan ke amfani da su, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.

Yadda aka sheƙe ƴan ta'addan

Edward Gabkwet ya ce an kai harin ne a maboyar ƴan ta’addan da ke ƙaramar hukumar Shiroro, a sansanin shugaban ƴan ta’adda, Malam Umar da wasu kwamandoji da ke yankin dajin Allawa.

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Hare-haren da aka kai an kai su ne bayan bayanai sun nuna tarin bukkoki a cikin bishiyoyi, tare ƴan ta'adda da ke ta yawo a wurin."

Kara karanta wannan

Sojoji sun sheke 'yan ta'adda 7 a wani sabon artabu a Sokoto

"Hakazalika, bayanan da aka samu sun tabbatar da cewa waɗannan ƴan ta'addan su ne ke da alhaki wajen kai hari ga sojoji a ƙauyen Bassa, da hare-haren bama-bamai a kan hanyar Pandogari-Allawa a ƙaramar hukumar."

Sojoji sun hallaka ƴan ta'adda

A wani labarin kuma, kun ji cewa sojojin Najeriya tare da haɗin gwiwar jami'an tsaro na farin kaya (DSS) sun hallaka ƴan ta'adda bakwai a jihar Sokoto.

Jami'an tsaron sun samu nasarar hallaka ƴan ta'addan ne a yankin Modachi na ƙaramar hukumar Isa ta jihar Sokoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel