'Kano, Yobe': An Saki Sunayen Jihohi 33 da Za Su Fuskanci Ambaliyar Ruwa a 2026

'Kano, Yobe': An Saki Sunayen Jihohi 33 da Za Su Fuskanci Ambaliyar Ruwa a 2026

  • Ministan albarkatun ruwa, Farfesa Joseph Utsev, ya sanar da cewa garuruwa 14,118 a ƙananan hukumomi 266 za su fuskanci barazanar ambaliya
  • Jihohi 33 da kuma babban birnin tarayya Abuja ne aka yi hasashen cewa ambaliyar za ta shafa tsakanin watan Afrilu zuwa Nuwamba, 2026
  • Manyan birane kamar Legas, Kano, Abuja, da Kaduna za su fuskanci ambaliya mai tsanani sakamakon toshewar magudanun ruwa a jihohinsu

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja – Gwamnatin Tarayya ta yi kira ga 'yan Najeriya da su shirya tsaf domin tunkarar ambaliyar ruwa da aka yi hasashen za ta afka wa jihohi 33 a cikin wannan shekara ta 2026.

Ministan albarkatun ruwa da tsabtace muhalli, Farfesa Joseph Terlumun Utsev, ne ya bayyana hakan yayin gabatar da rahoton hasashen ambaliya na shekara-shekara a yau Laraba, 15 ga Afrilu, 2026.

Kara karanta wannan

Abubakar Malami: Shari'ar tsohon Ministan Buhari ta dauki sabon salo a kotu

Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa jihohi 33 za su fuskanci ambaliyar ruwa mai tsanani a 2026
Wani gari ya gamu da ambaliyar ruwa, jami'ai na kokarin ceto wadanda suka makale. Hoto: Sani Hamza/Staff
Source: Original

Jihohi 33 za su fuskanci ambaliya a 2026

Ministan ya bayyana cewa garuruwa 14,118 da ke cikin ƙananan hukumomi 266 suna cikin babban haɗarin ambaliya, kamar yadda rahoton Daily Trust ya nuna.

A cewar Farfesa Joseph Terlumun Utsev:

"Fadakar da mutane tun da wuri na taimaka wa wajen ceton rayuka da dukiyoyi, tare da rage asarar tattalin arziki."

Rahoton ya nuna cewa ambaliyar za ta kasance kashi uku, inda wasu yankuna za su fuskanci ambaliya mai tsanani, wasu kuma matsakaiciya.

Ambaliya mai tsanani za ta shafi jihohi 33 ciki har da Adamawa, Bauchi, Borno, Jigawa, Kaduna, Kano, Kebbi, Kogi, Legas, Sokoto, Taraba, Yobe, da Zamfara.

Ambaliya za ta kuma shafi manyan birane kamar Abuja, Kano, Legas, Kaduna, Ibadan, Benin, da Fatakwal, in da za su fuskanci barazanar saboda rashin kyawun magudanun ruwa da yawan ruwan sama.

Sannan akwai ambaliyar gabar teku, inda jihohi kamar Bayelsa, Delta, Legas, Rivers, da Ondo za su fuskanci ambaliya sakamakon hauhawar ruwa a tekunan da ke kewaye da su.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta fayyace gaskiya game da 'kisan fararen hula' a Borno

Lokutan da ambaliya za ta fi tsanani

Farfesa Utsev ya fayyace cewa za a fara ganin alamun ambaliyar ne tun daga wannan watan na Afrilu har zuwa watan Nuwamba, 2026, in ji rahoton jaridar Tribune.

Rahoton ya nuna cewa garuruwa 9,021 za su shiga haɗarin ambaliya a watan Afrilu zuwa Yuni, yayin da garuruwa 14,158 za su gamu da ambaliyar daga Yuli zuwa satumba, lokacin da ambaliyar za ta yi muni sosai.

Hakazalika, ana sa ran garuruwa 11,575 za su ci gaba da fuskantar ambaliyar ruwa daga Oktoba har zuwa lokacin da ake sa ran daminar za ta zo karshe a watan Nuwamba.

Ministan albarkatun ruwa ya bukaci gwamnatin jihohi da su dauki matakan gaggawa na kare garuruwa daga ambaliya.
Ministan albarkatun ruwa da tsabtar muhalli, Joseph Terlumun Utsev ya na jawabi a taron kaddamar da shirin SPIN a Abuja. Hoto: @JosephUtsev
Source: Twitter

Kiran gwamnati ga jihohi da manoma

Ministan ya jaddada cewa wannan ambaliya za ta shafi harkar noma, kiwon dabbobi, gine-gine, da kuma tattalin arzikin ƙasa baki ɗaya. Don haka, ya yi kira ga gwamnatocin jihohi da hukumomin agajin gaggawa da su fara ɗaukar matakan kariya tun yanzu.

Ya buƙaci shugabannin al'umma da manoma su yi amfani da bayanan rahoton AFO domin kaurace wa yankunan da ruwa zai iya cinye su, sannan su tabbatar an share magudanun ruwa a birane domin rage radadin ambaliyar.

Kara karanta wannan

Pantami ya yi maganar siyasa, ya haska dalilin da zai sanya a zabe shi a 2027

Ambaliya ta yi ajalin mutane a Zaria

A wani labari, mun ruwaito cewa, mutane uku sun mutu yayin da aka rasa wasu biyu sakamakon ambaliyar ruwa da ta biyo bayan ruwan sama a Zariya, jihar Kaduna.

An gano gawar Fatima Sani Danmarke da wani dalibi Yusuf Surajo Tudun Wada, yayin da ake cigaba da neman wata yarinya ‘yar shekara uku.

Rahotanni sun bayyana cewa ambaliyar ruwan ta tafi da wani mazaunin unguwar Tudun Jukun da ya yi yunkurin ceto Fatima da ‘yar uwarta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com