Naira Ta Gama Tashin Gishirin Andrew, Dalar Amurka Ta Sake Harbawa a Najeriya

Naira Ta Gama Tashin Gishirin Andrew, Dalar Amurka Ta Sake Harbawa a Najeriya

  • Labaran da muka samu daga wurare dabam-dabam sun bayyana cewa kudin Najeriya watau Naira ya fadi a kasuwa
  • Kwanaki bayan Dalar Amurka ta fado sosai, sai aka ji Naira ta cigaba da rasa kimarta a kasuwar canji da kuma bankuna
  • ‘Yan kasuwar canji suna saida Dala a kan kusan N1, 400, wannan ya maida murnar da ‘yan Najeriya suka fara zuwa ciki

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Daraja da kimar kudin Najeriya watau Naira yana ta karyewa bayan ana murnar ya farfado a can kwanakin baya.

Rahotanni sun bayyana cewa Dalar Amurka ta tashi a kasuwanni canji na bayan fage da kuma a hannun bankunan kasar.

Naira da Dala
Naira ta karye a kan Dala a kasuwar canji a Najeriya Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Nawa ake canza Naira a kan Dala?

Kara karanta wannan

Shirin ba ɗalibai rancen kuɗi; Tinubu ya naɗa Jim Ovia a matsayin shugaban NELFund

Bayanan da aka samu daga shafin Naira Rates a shafin X da aka fi sani da Twitter ya nuna Dala ta dawo N1, 250.527.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A safiyar Juma’ar, an saida Pounds na Birtaniya a kan N1528 sai kuma kudin Euro na kasashen Turai a kan N1, 337.59.

Dala ta dawo tsakanin N1300 - N1400

The Cable ta ce Naira ta karye zuwa N1, 320 a kan duk Dala zuwa tsakiyar makon nan.

Abin da hakan yake nufi shi ne kudin kasar na Naira ya karye da 1.54% daga N1, 300 da aka canji Dalar Amurka kafin yanzu.

A hannun ‘yan canji da ke kasuwannin BDC, an rika sayen Dala a kan kusan N1, 300 sannan a saida da ribar sama da N50.

Farashin Naira da Dala a FMDQ

A kafar FMDQ da ake cinikin kudin kasashen waje, an saye Dala ne a N1, 410 a jiya.

Kara karanta wannan

Ondo 2024: Jam'iyyar PDP ta tsayar da dan takarar gwamna da zai kara da Aiyedatiwa

Rahoton ya ce ga masu bukatar sayen kudin kasar Amurkan, sai sun biya akalla N1, 051 zuwa yammacin ranar Juma’ar nan.

Naira ta tashi, ta sauka a kasuwa

Kwanakin baya Dalar ta karye zuwa kusan N1, 000 a kasuwanni da bankuna, hakan ya sa aka fara tunanin farfadowar Naira.

Ruguzowar kimar Naira a yau ya sake jawo alamar tambaya a kan dabarun da Yemi Cordoso ya fito da su bayan an nada shi.

Wasu masana tattalin arziki sun bayyana cewa dama zai yi wahala darajar Naira ta dade a haka, kimar kudin zai sake ruguzowa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng