Wutar Rikici Ta Fara Tashi a Jam'iyyar APC, Yilwatda Ya Gargadi Tsofaffin Ƴan PDP

Wutar Rikici Ta Fara Tashi a Jam'iyyar APC, Yilwatda Ya Gargadi Tsofaffin Ƴan PDP

  • Shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya yi magana game da zargin sababbin zuwa za su kwace ikon ragamar jam'iyyar
  • Yilwatda ya ce dole ne masu sababbin shiga su nuna takardar murabus daga tsohuwar jam’iyyar su kafin a ba su wani muƙami a APC
  • Ya kuma fadi irin alakar da ke tsakanin APC da Ministan Abuja, Nyesom Wike wanda ke aiki da gwamnatin Bola Tinubu, amma yana PDP

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja – Shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya bayyana cewa ba za su amince wa tsofaffin mambobin PDP da suka sauya sheƙa su karɓe madafun ikon jam’iyyar ba tare da la’akari da tsofaffin mambobi ba.

Yilwatda ya bayyana hakan ne a ranar Talata, 14 ga Afrilu, 2026, yayin wani taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC na shiyyar babban birnin tarayya, Abuja.

Kara karanta wannan

APC a Adamawa ta rikice, mai neman takarar gwamna ya fice daga jam'iyya

APC ta ba za ta bari sababbin shiga jam'iyyar su kwace ragamar iko ba.
Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Nentawe Yilwatda, da tutar jam'iyyar APC. Hoto: @OfficialAPCNg
Source: Twitter

An raba aya da tsakuwa a mambobin APC

Wannan bayani na zuwa ne a daidai lokacin da rahotanni ke nuna cewa tsofaffin jiga-jigan PDP da suka dawo APC suna ƙoƙarin mamaye rassan jam’iyyar domin tabbatar da samun tikitin takara a zaɓe mai zuwa, in ji rahoton The Guardian.

Shugaban jam’iyyar ya nanata cewa ko da yake ana maraba da kowa, amma ba za a bari bakin shigowa su zo su kori waɗanda suka gina jam’iyyar ba.

Ya bayyana cewa:

"Ba za mu bari mutanen da suka sauya sheƙa su zo su karɓe jam’iyyar ba. Su sani cewa sun tarar da mutane a cikin gidan da aka gina shi da ƙyar da jibin goshi. Idan da ba a gina gidan ba, da ba za su shiga ba."

Domin tabbatar da bin doka, Yilwatda ya gindaya sharaɗin cewa dole ne sababbin shiga jam’iyyar su nuna takardar murabus ɗinsu daga tsohuwar jam’iyyarsu kafin neman mukami.

Kara karanta wannan

Jigon ADC ya 'gano' halin da APC ke ciki, ya fadi hadin da zai kai Tinubu ƙasa a 2027

Alakar jam'iyyar APC da Wike

Game da rahotannin cewa magoya bayan Ministan Abuja, Nyesom Wike, suna ta kwarara zuwa cikin APC, Farfesa Yilwatda ya ba da haske kan dangantakar jam’iyyar da Ministan.

Ya jaddada cewa Wike ba mamba ne na APC ba, kuma jam’iyyar ba ta taɓa tuntuɓarsa kan wani al’amari da ya shafi APC ba, in ji rahoton The Nation.

"Ministan Abuja ba mamba ne na APC ba. Mun dai san cewa ya rubuta wa jam’iyyar PDP wasiƙa a farkon wannan gwamnati, kuma PDP ta ba shi izinin yin aiki a cikin gwamnatinmu," in ji Yilwatda.
Nentawe Yilwatda ya ce dole sababbin shiga APC su nuna takardar murabus dinsu daga tsofaffin jam'iyyu kafin samun mukami.
Shugaban jam'iyyar APC ta kasa, Nentawe Yilwatda ya na jawabi a wani taro a Abuja. Hoto: @OfficialAPCNg
Source: Twitter

Tsarin da ya ba Yilwatda damar shugabantar APC

Ya ƙara da cewa APC tana da tsari na tafiya da kowa ba tare da bambanci ba, yana mai buga misali da kansa a matsayin wanda ya fito daga ƙabilar tsirarun mutane da ya samu damar shugabantar jam’iyyar saboda wannan tsari.

"Ina shugabantar jam'iyyar nan ne saboda tsarinta na tafiya da kowa. Ba don wannan tsari ba, da ba zan iya rike wannan mukami ba, saboda na fito ne daga kabilar da ta wanzu a kananan hukumomi biyu kawai a kasar nan."

Kara karanta wannan

Gwamna Inuwa Yahaya ya ce rufin asirin jama'a na cikin nasarar APC a 2027

- Farfesa Nentawe Yilwatda.

Haka kuma, ya jaddada cewa duk wanda ya shafe shekaru takwas yana riƙe da muƙami ɗaya, dole ne ya sauka ko ya canza muƙami, kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada.

Ana tilasta wa ma’aikatan gwamnati shiga APC?

A wani labari, mun ruwaito cewa, jam’iyyar APC ta fusata da ake yada rahotanni kan tilasta wa ma'akatan gwamnatin Najeriya shiga cikinta.

Jam'iyyar ta ƙaryata zargin da jam’iyyar ADC ta yi na cewa ana tilasta wa ma’aikatan gwamnati shiga rajistar mambobin APC ta hanyar intanet.

APC ta ce wannan zargi na daga cikin yaɗa bayanan ƙarya da ADC ke yi, ciki har da yada wata takardar rajistar APC ta bogi wadda ake ƙoƙarin nuna cewa wani sanannen ɗan ta’adda ya yi rajista da jam’iyyar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com