Abin da zai Hana El Rufai Shaƙar Iskar Ƴanci duk da Kotu Ta Bayar da Belinsa

Abin da zai Hana El Rufai Shaƙar Iskar Ƴanci duk da Kotu Ta Bayar da Belinsa

  • Har yanzu tsohon gwamna Nasir El-Rufai na hannu bayan kotu tarayya a Kaduna ta bayar da belinsa kan zargin da ake yi masa
  • An sa sharudda masu tsauri, ciki har da kudin beli Naira miliyan 200 da kawo wanda zai tsaya masa kafin a sake shi
  • Duk da beli, Malam El-Rufai zai ci gaba da zama a hannun ICPC har sai ya cika dukkannin sharuddan da kuma wasu dalilai

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kaduna – Kotun Tarayya da ke Kaduna ta amince da beli ga tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, a shari’ar da hukumar yaki da cin hanci da rashawa (ICPC) ke tuhumarsa da aikata laifuffuka.

Alkalin kotun, Mai shari’a Rilwanu Aikawa, ne ya yanke hukuncin a ranar Talata, 14 ga watan Afrilu, 2026 bayan ya saurari hujjojin bangaren masu kara da kuma na masu kare wanda ake zargi.

Kara karanta wannan

Nasir El-Rufai ya samu beli bayan dogon lokaci ana shari'a a kotu

An ba da belin Nasir El-Rufa'i
Tsohon gwamnan Kaduna yana dab da shiga kotu a ranar Talata, 14 ga watan Afrilu, 2026 Hoto: ADC Kwankwasiyya
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa kotun ta amince a ba shi beli kan kudi Naira miliyan 200, tare da sharudda da dama da dole ne ya cika kafin ya samu ‘yanci.

Har yanzu Nasir El-Rufa'i na tsare

Jaridar Punch ta wallafa cewa sai dai kotun ta umarci cewa El-Rufai zai ci gaba da zama a tsare a hannun ICPC har sai ya cika dukkanin sharuddan belin da aka gindaya masa.

Daga cikin sharuddan akwai hana shi yin wata magana a bainar jama’a kan shari’ar, tare da wajabcin halartar duk zaman kotu da za a yi a nan gaba.

Wani makusancin tsohon gwamnan ya bayyana cewa an gindaya masa kusan sharudda 10, daga ciki har da samar da wanda zai tsaya masa da ke da kadara da kuma mukamin gargajiya.

Hukumar ICPC ta gurfanar da El-Rufai a gaban kotu kan tuhume-tuhume guda tara da suka shafi zargin almundahana da cin zarafin ofis.

Kara karanta wannan

Dalilin kotun Kaduna na sake 'dage shari'ar neman belin Nasir El Rufa'i

Daya daga cikin manyan zarge-zargen shi ne ya sa gwamnatin Kaduna ta fitar da kusan Naira biliyan 11 zuwa wani kamfani da ba a yi rajistarsa ba domin aikin layin dogo na cikin gari, wanda ba a aiwatar da shi ba.

Sai dai El-Rufai ya musanta dukkanin zarge-zargen da hukumar yaki da rashawa ta ICPC ke yi masa a gaban kotun.

Dalilin ci gaba da tsare El-Rufa'i

An tsare El-Rufa'i tun ranar 19 ga watan Fabrairu na shekarar 2026 bayan wata shari’a da hukumar EFCC ta gabatar, duk da cewa an taba sakinsa na dan lokaci domin halartar jana’izar mahaifiyarsa.

Wani lauya mai zaman kansa a Kaduna, Barista El Zubair Abubakar ya bayyana cewa akwai yiwuwar El-Rufai ba zai fita daga tsare nan take ba duk da samun beli.

A cewar Barista El Zubair Abubakar, hakan na da nasaba da kasancewar akwai shari’o’i biyu daban-daban da ake yi masa a kotuna biyu.

El-Rufa'i zai ci gaba da zama a tsare
Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i a kofar shiga kotun tarayya da ke Kaduna Hoto: Tinubu Reporters
Source: Facebook

Ya ce duk da cewa Kotun Tarayya ta ba shi beli, akwai wata shari’a da ke gaban Kotun Jihar Kaduna wadda har yanzu ba a yanke hukuncin beli a kanta ba.

Saboda haka, zai ci gaba da zama a tsare har sai kotun jihar ta yanke hukunci kan bukatar belin, tare da cika sharuddan da dukkan kotunan suka gindaya masa.

Kara karanta wannan

Kotu ta sanya lokacin yanke hukunci kan bukatar belin El Rufai

Barista El Zubair Abubakar ya kara da cewa, idan aka yi la’akari da irin laifuffukan da ake zargin, akwai yiwuwar kotu za ta amince da beli a shari’ar ta biyu, amma sai an jira hukunci.

An ji gaskiya kan takarar El-Rufa'i

A wani labarin, mun wallafa cewa wani jigo a jam'iyyar ADC kuma na kusa da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya yi magana game siyasar tsohon ministan a 2027.

Hayatudeen Lawal Makarfi ya bayyana cewa El-Rufai yana shirin tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027, ya ce shirye-shirye sun yi nisa wajen ganin hakan ta tabbata .

Sai dai kuma, Muyiwa Adekeye, mai magana da yawun El-Rufai, ya karyata wannan ikirari na Hayatudeen, tare da fayyace gaskiya a kan ko mai gidansa zai nemi kujerar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng