Najeriya Na Asarar N1.29tr Duk Shekara Saboda Satar Danyen Mai, Abbas Tajudeen

Najeriya Na Asarar N1.29tr Duk Shekara Saboda Satar Danyen Mai, Abbas Tajudeen

  • Abbas Tajudeen ya bayyana asarar da Najeriya take tafkawa duk shekara sakamakon satar ɗanyen man fetur da fasa bututun mai
  • Kakakin majalisar wakilan ya bayyana cewa a kullum Najeriya na asarar gangar mai 300,000 wanda ƙiyasin kuɗinsu ya kai N1.29 a shekara
  • A yayin da yake yabawa rundunar sojojin ruwan Najeriya kan matakan da ɗauka wajen daƙile matsalar, ya kuma buƙace su da su ƙara ƙaimi wajen kawo ƙarshenta

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Ribas - Kakakin majalisar wakilai, Abbas Tajudeen, ya ce Najeriya na asarar Naira tiriliyan 1.29 a duk shekara sakamakon satar mai, fasa bututun mai da sauran laifuka.

Abbas Tajudeen ya bayyana cewa Najeriya tana asarar kusan gangar ɗanyen mai 300,000 kowace rana saboda sata.

Kara karanta wannan

Zulum ya ba sojoji shawara kan hanyar da za a kawo karshen rashin tsaro a Borno

Satar danyen mai na jawowa Najeriya asara
Abbas Tajudeen ya koka kan satar danyen mai a Najeriya Hoto: Abbas Tajudeen
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ce kakakin majalisar wakilan ya bayyana hakan ne ta hannun shugaban kwamitin tsaro na majalisa, Babajimi Benson, a wajen ƙaddamar da cibiyar horas da sojojin ruwa a Eleme, jihar Ribas a ranar Juma’a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce lamarin ya haifar da ƙalubale ga rundunar sojojin ruwan Najeriya domin ta tashi tsaye wajen gudanar da aikinta na bayar da gudunmawa ga ci gaban tattalin arziƙin ƙasa.

Wace shawara ya ba sojoji?

Ya buƙaci sojojin ruwan Najeriya da su kare tare da tsare martabar yankin ruwan Najeriya daga duk wata barazana, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.

A kalamansa:

"Abin takaici, ana ƙiyasin cewa Najeriya tana asarar sama da ganga 300,000 na ɗanyen mai a kullum, ta hanyar satar mai, fasa bututun mai da sauran laifuka."
"Hakan ya haifar da asarar kuɗaɗen shiga da aka ƙiyasta sun kai Naira tiriliyan 1.29 a duk shekara."

Kara karanta wannan

Daga karshe Ganduje ya bayyana wadanda suka kitsa dakatar da shi daga jam'iyyar APC

Saboda haka, damuwa da na yi da asarar da satar mai ke jawowa Najeriya, na kafa kwamiti na musamman kan satar ɗanyen mai a ranar, 22 ga watan Nuwamba 2023, domin zaƙulo matakan da ya kamata a ɗauka.
"Na yabawa rundunar sojojin ruwa bisa matakan da ta ɗauka ya zuwa yanzu, sannan ina roƙonsu da su ci gaba da yin hakan."

An gano rijiyoyin satar mai

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun gano wasu rijiyoyin mai 42 da ake satar ɗanyen mai waɗanda ba a san da su.

Sojojin sun gano waɗannan rijiyoyin man fetur ɗin ne a wani ƙauye mai suna Rumuekpe da ke a ƙaramar hukumar Emohua ta jihar Ribas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel