Sojoji Sun Sheke 'Yan Ta'adda 7 a Wani Sabon Artabu a Sokoto

Sojoji Sun Sheke 'Yan Ta'adda 7 a Wani Sabon Artabu a Sokoto

  • Dakarun rundunar sojojin Najeriya sun samu nasarar daƙile wani yunƙurin kai harin ta'addanci da ƴan ta'adda suka yi a jihar Sokoto
  • Sojojin tare da haɗin gwiwar jami'an tsaro na farin kaya (DSS) sun sheƙe ƴan ta'adda bakwai a yankin Modachi na ƙaramar hukumar Isa a jihar
  • Bayan tura ƴan ta'addan zuwa barzahu, jami'an tsaron sun kuma ƙwato bindigu da adduna a hannun miyagun masu tada ƙayar bayan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Sokoto - Rundunar sojojin Najeriya tare da haɗin gwiwar jami'an tsaro na farin kaya (DSS) sun hallaka ƴan ta'adda bakwai a jihar Sokoto.

Jami'an tsaron sun samu nasarar hallaka ƴan ta'addan ne a yankin Modachi na ƙaramar hukumar Isa ta jihar Sokoto.

Kara karanta wannan

Rundunar sojojin sama ta ragargaji 'yan ta'adda a jihar Neja

Sojoji sun sheke 'yan ta'adda
Sojoji sun hallaka 'yan ta'adda a Sokoto Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Facebook

Hakan na ƙunshe ne a cikin sanarwar da rundunar sojojin Najeriya ta fitar a shafinta na X (wanda a baya aka fi sani da Twitter), a ranar Juma'a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojoji sun sheƙe ƴan ta'adda

Dakarun sojojin sun hallaka ƴan ta'addan ne lokacin da suka daƙile wani yunkurin kai hari da suka yi bayan sun samu kiran gaggawa.

Sanarwar ta jaddada cewa, sojojin a wani samame na haɗin gwiwa sun kashe bakwai daga cikin ƴan ta'addan tare da kwato manyan makamai daga ƴan ta'addan da aka kashe.

Jami’an tsaron Najeriya sun yi artabu da ƴan ta’addan da ke kan hanyar wucewa kan babura da dama inda suka yi nasarar tura guda bakwai daga cikinsu zuwa barzahu.

Rundunar ta bayyana cewa sojojin sun kuma ƙwato bindigogi ƙirar AK-47 guda bakwai, babura huɗu, wayoyin hannu guda biyu da adduna huɗu daga hannun ƴan ta’addan.

Kara karanta wannan

Bam ya hallaka jami'an CJTF 5 a jihar Borno, wasu sun samu raunuka

Legit Hausa ta samu jin ta bakin wani mazaunin jihar Sokoto mai suna Malam Dalhat wanda ya yaba da wannan nasarar da jami'an sojojin suka samu.

Ya bayyana cewa sun yi bajinta matuƙa inda ya yi kira a gare su da su ƙara ƙaimi wajen kakkaɓe ƴan ta'addan da suka addabi mutane.

A kalamansa:

"Eh lallai wannan abin a yaba ne sosai, tabbas sun yi matuƙar ƙoƙari kuma sun cancanci yabo. Muna fatan za su ci gaba da ƙoƙarin da suke yi na kawo ƙarshen ƴan ta'adda."

Sojoji sun hallaka ƴan ta'adda

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojoji na runduna ta 6 da ake kira 'Whirl stroke' sun kashe ƴan ta'adda biyu a jihar Taraba.

Dakarun sojojin sun samu wannan nasarar ne yayin da suka dakile wani hari a ƙauyen Kweserti da ke a ƙaramar hukumar Ussa ta jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel